News

BIDIYO: Yadda Kwankwaso Ya Sauka A Lagos Kan Dai Daito Da Gwamnati Game Da Batun Kulle Kasuwar Alaba Rago

BIDIYO: Yadda Kwankwaso Ya Sauka A Lagos Kan Dai Daito Da Gwamnati Game Da Batun Kulle Kasuwar Alaba Rago

Kwankwaso ya dira legas don daidaito da gwamnati kan rushe kasuwar alaba

Daga Tukur Sani Kwasara

“Rushe babban kasuwar Alabar rago dake legas; kwankwaso ya dira birnin legas domin daidaitawa da gwamnatin jihar”

“Yanzu haka, rahotonnin da suke riskan mu cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sauka a jihar Legas domin ganawa da Gwamna jihar akan batun rushe kasauwar alabar Rago.

“Mutanen Alaba Rago Kenan Yayin Godiyarsu ga Sanata Kwankwaso Akan Aniyarsa ta ganin gwamnatin Legas ta hakura da rusa Babbar Kasuwar Alaba Rago Dake Birnin Legas.”

GWAMNATIN JAHAR LAGOS TA BAIWA KASUWAR ALABA RAGO WA’ADIN SATI BIYU SU TASHI DOMIN YIN GYARA.

DUK INDA TARON BAHAUSHE YAKE A LAGOS HAKA ZAKAGANSA TAMKAR KARA ZUBE BABU TSARI.

Akwai wani abu daya kamata mutanen Arewa su sani. So dayawa idan aka dauki wani mataki akan yan arewa sai muyita cece kuce da nuna rashin jin dadi. Amma laifin waye?

Wannan kasuwar Ta (ALABA RAGO) Kasuwa ce mai dadadden tarihi wadda ta tara yan kasuwa daga yankin Arewa da kasashen ketare kamar Ghana dakuma togo da Benim republic.

Itadai wannan kasuwar ana sauke dukiya ta miliyoyin kudi. Akalla kusan kullum za’a sauke Hatsi da dabbobi na kusan miliyan 300 zuwa 500. Ko ince a sati.

Tareda haka bazaka iya shiga wurin cikin natsuwa da kwanciyar hankali ba. Saboda irin lalacewar wurin da rashin tsari na kasuwar. Mafi yawancin mutanenmu basuda mallakar wurarenda suke sana’a saboda tunanin wai ba zama sukazo ba. Gashi tsawon shekaru suna zaune a wurin.

Rashin tsari da kyautata wurin yasa masu laifuffuka daban daban sukan samu malaba a irin wuraren nan. Haka tunanin bahaushe yake a lagos nayin rayuwa babu tsari babu zamanantawa. Shiyasa koda yaushe muka kasa samun cigabanda yadace. Kuma akemana yadda akeso.

Idan ka tsallaka dayan bangaren na kasuwar nan ne( ALABA INTERNATIONAL) wato kasuwar kayan wuta da sauran abubuwa. Wannan bangaren Inyamarai ne suke zaune wurin suke kasuwanci. Dayawansu sun mallaki shagona na kansu da plaza plaza da gidaje a yankin. Zaiyi wahala kaga wuri a lalace cikin kazanta kamar kasuwar ALABA RAGO ta mutanenmu hausawa. Hakan yasa basa fuskantar barazana daga gwamnati akowane lokaci.

Ga Bidiyon Nan Ku Kalla

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button