BIDIYO: Yadda Kotu A Saudia Ta Fara Sauraren Shari’ar Masu Daga Fastocin Yan Siyasa A Dakin Ka’aba
Saudiya ta tasa keyar Yan Nijeriyan da suka daga fatsan Yan siyasa gidan yari.
“Rahotonni daga majiyoyi, sun shaida mana cewa! an tasa keyar ‘Yan Nijeriya wadanda suka daga fastocin Yan takaran shugabancin Nijeriya na Atiku da Tinubu a gaban ka’aba gidan yari dake kasar saudiyya har sai umma ta gani.”
Bugu da kari har izuwa yanzu dai kotun tace a dai a ajiye su har sai sharia ta waiwaye su, nan dai aka rufe shafinsu na shari’an.”
“Sai dai an dunga samun wasu sakonni daga Nijeriya zuwa kasar saudiya din, da nufin kotu ta bayar da belin su akan ko mawane.
“inda wakilin namu dan Nijeriya amma mazaunin kasar saudiya ke shaidawa Jaridar Alfijir Hausa din.
Lallai Hukumar saudiyan tayi barin tamba da manufar bayar da belin nasu, inda hukumar ta saudiya tace al’amarinma dai yana hannun shari’a ne ba hannun su ba.”
Ga Bidiyon