News

BIDIYO: Yadda Jami’an Ƴan Sanda Suka Sami Nasarar Kuɓutar Da Yara 113 Da Ga Gidan Mari A Kano

Ƴan Sanda sun kuɓutar da yara 113 da ga gidan mari a Kano

Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Kano ta gano wani gidan mari da a ke gudanar da shi ba bisa ƙa’ida ba, inda ta tserar da yara 113 da ga ciki.

Rundunar ta ce ta bankaɗo gidan ne bayan da ta samu rahoto da ga wasu yara da su ka samu hanya su ka tsere da ga gidan da ke Unguwar Wailari, Ƙaramar Hukumar Kumbotso a cikin garin Kano.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a jiya Talata, rundunar ta ce da ga samun rahoton, Kwamishinan Ƴan Sanda Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bada umarnin a je a bincika.

Ya ƙara da cewa bayan jami’an sintirin sirri sun je sun tabbatar da rahoton, sai rundunar ta ɗora a gidan inda ta tarar da yara 113 inda a ka kulle su kuma a ke hana musu azaba har mutum ɗaya ya rasa ransa.

Kiyawa ya ƙara da cewa sun kama wani Musa Safiyanu, mai shekara 55 kuma shine mai gidan marin tare da masu taimaka masa su 4.

Yayin bincikar wandanda ake zargi, in ji Kiyawa, sun bayyana cewa gidan marin ya fi shekara goma suna gudanar dashi duk da cewa gwamnati ta haramta.

SP Kiyawa yace wasu daga cikin ƴan marin a ɗaure suke cikin sarƙa, suna ɗauke da raunuka daban-daban, in da ya ƙara da cewa tuni a ka garzaya da su asibitin Murtala domin basu taimako sannan an mika su ga hannun gwamnati.

Ya tabbatarwa da mutanen Jahar Kano za a hukunta wandanda aka kama da zarar Hukumar ‘Yan Sanda ta kammala binciken ta.

https://youtu.be/6cJSo2Bi0IE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button