Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Kirkiro Da Ma’aikatar Kula Da Harkokin Fulani – Bello Badejo
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kyautal Hore na Kasa, Abdullahi Bello Badejo ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta samar da ma’aikatar kula da harkokin Fulani.
Shugban ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kamma wani da taro da ya shafi Fulani mai taken ‘Fulani ina mafita.’
Ya ce taron yana da matukar muhimmanci a al’amuran da suka shafi Fulani, kuma taron ya gudana ne har kashi biyu.
A cewarsa, Fulanin Nijeriya suna fuskanta matsaloli daban-daban, shi ya sa suka ga ya fi dacewa su nemi Fulani su nuna masu cewa suna tare da su dari bisa dari tare da nuna musu cewa lalle suna da shugabanci da kuma wakilci, domin kar su dauka ba su da shugabanci ko kuma wakilci.
Ya kara da cewa sun nemi masu ruwa da tsaki wanda suke da ilimin zamani daga cikin Fulani da masana kan kiwon dabbobi a Nijeriya wadanda aka yi su shekaru da suka gabata, domin su bayar da shawarwari kan matsalolin da suka shafi Fulani a Nijeriya.
Ya nuna farin cikinsa bisa amsar goron gayyata na masu ruwa da tsaki kuma har sun tofa albarkacin bakinsu a wurin wannan taro
Shugaban kungiyar ya ce babu wani da zai kasance shugaba ko sarki ya ji dadi ana rikici a jiharsa ko yankinsa.
Ya ce, “Wannan shi ya sa muke ganin wasu gwamnoni ba laifinsu ba ne kuma shi ma shugaban kasa ba laifinsa ba ne ake ta rigima, musamman ta Fulani da wasu kabilu, domin gwamnati tana da fadi.
“Mu a kungiyan Miyetti Allah Kautal Hore ya za mu yi mu shigo domin taimaka wa gwamnati da kuma hukumomin tsaro wajen dakile rikici a tsakanin Fulani da sauran kabilu.