BIDIYO: Wasu Fusatattun Matasa Sun Kona Motar Dan Takarar Gwamnan Jahar Katsina.
Wasu fusatattun matasa sun ƙona motocin yaƙin neman zaɓen Ɗan takarar kujerar Gwamnan jihar Katsina a jam’iyyar APC Dr. Mustapha Inuwa, a garin Charanchi da ke jihar Katsina.
Kamar Yadda Zakuji Cikakken Rahoton Acikin Bidiyon Dake Kasa.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ayarin motocin suke kan hanyar zuwa karamar hukumar Kankia domin halartar babban taron da Jam’iyyar APC ta shirya na bada tuta ga ƴan takarkarin ciyamomin ƙananan hukumomi na jihar baki ɗaya.
Shin A ganinku Jam’iyyar APC zata ƙara yin wani tasiri a zaɓen 2023 idan Allah ya kai mu.
Ga Dai Cikakken Rahoton Ku Kalla.