BIDIYO: Lauyoyi tara sun kai Safara’u, da Gwanja da Murja ƙara Kotun Shari’ar Musulunci
Wasu lauyoyi guda tara sun kai wasu mutum goma ƙara waɗanda suka shahara a shafin Tiktok.
Mai magana da yawun kotunan Jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ne ya tabbatar wa BBC da lamarin inda ya ce lauyoyin sun rubuta takardar koken inda suka ce mutane goman na ƙoƙarin ɓata tarbiyya ta hanyar yin waƙoƙin batsa da baɗala.
Lauyoyin sun shigar da ƙarar ne a gaban kotun ɗaukaka ƙara ta Shari’ar Musulunci da take Bichi inda daga baya kotun ta buƙaci kwamihsinan ƴan sanda na jihar da a lalubo mutanen a gudanar da bincike a kansu.
Cikin mutanen da suka sharara a tiktok da aka kai ƙararsu akwai Mista 442 da Safara’u da Dan Maraya da Amude Booth da Kawu Dan Saraki.
Sauran sun haɗa da Ado Isa Gwanja da Murja Ibrahim Kunya da Ummi Shakira da Samha M Inuwa da kuma Babiyana.
BBC ta tuntuɓi Ado Gwanja don jin amma wayarsa ba ta shiga, sannan bai amsa saƙon da aka tura masa ba da zummar son yin magana da shi ba.
Sai dai mun samu Mr 442 wanda ya ce tashi kawai ya yi daga bacci ya ga takardar na yawo.
“A yanzu babu abin da zan ce tun da batu ne na shari’a, amma na miƙa wa lauyana wuƙa da nama.”
Haka su ma sauran waɗanda aka kai su ƙarar duk ba a same su ba zuwa lokacin wallafa wannan labarin.
Ko a kwanakin baya dai sai da aka yi ta ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta kan cewa hukumar Hisbah a Kano tana neman Safara’u, sai dai a wata hira da BBC, Safara’un ta ce ba ta san da batun ba.
Haka kuma akwai waƙar da Ado Gwanja ya yi a baya-bayan nan ta “A Sosa”, wadda ta yi matuƙar jawo ce-ce-ku-ce da raddi har daga malamai.
Ita ma Murja Kunya wadda ake yawan ganinta a Tiktok tana yawan zagi da ashariya inda ko a kwanakin baya sai da ta yi bidiyo a Tiktok tana ɗura wa wani ashar kan ya yi mata ƙarya da cewa ta mutu.