Kiristoci Sunyi Zanga Zanga Kan Kisan Devorah Samuel Wadda Ta Rasa Ranta Sakamakon Batanci Ga Annabi
Muna Kalubalantar Rashin Bin Doka Wajen Hukumta Wadanda Suka Kashe Deborah-CAN Flato
Kungiyar hadin kan Kirista a Najeriya-CAN, reshen jahar Filato ta bukaci a rika yin hukunci kan duk wadanda suka aikata ba daidai ba, don samar da adalci ga kowa.
Kungiyar ta CAN tun farko ta umurci rassanta na jihohi su gudanar da zanga-zangar lumana ne don gabatar da sakon rashin jin dadi da kisan da wasu matasa su ka yi wa wata daliba mai suna Deborah Samuel a kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari a Sakkwato, bisa zarginta da sabo.
Shugaban kungiyar CAN a jihar Filato, Rabaran Father Polycarp Lubo yace rashin bin doka wajen aiwatar da kisan na Deborah, shine suke kalubalanta da jan hankalin hukumomi su yi adalci.
A cewar Rabaran Dakta Gideon Par-Malam, bai kamata irin wadannan kashe-kashe su ci gaba da aukuwa a Najeriya ba.
Ita ma Madam Edna Caleb Gochin wacce ta halarci gangamin ta ja hankalin matasa ne da su daina amfani da kafar sada zumunta wajen yada kalaman kiyayya.
Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, dakarun dake wanzad da zaman lafiya da Civil Defense sun bada kyakkawan tsaro a harabar ofishin na CAN har aka kammala gudanar da gangamin ba tare da matsala ba.
https://youtu.be/yYL1HZ0kpUE