Religion

BIDIYO: Kiristoci Sun Karrama Mahaddacin Al’qur’ani Mai Girma A Jahar Kaduna

BIDIYO: Kiristoci Sun Karrama Mahaddacin Al’qur’ani Mai Girma A Jahar Kaduna

KADUNA: Malaman Addinin Kirista Sun Karrama Wani Matashi Da Ya Haddace Al-Qur’ani

A yayin da majalissar dinkin duniya ta ware ranakun 13 zuwa 16 a matsayin makon fahimtar juna tsakanin mabanbanta addinai da kabilu, malaman addinin Kirista a jahar Kaduna sun karrama wani matashi da ya haddace al-qur’ani.

Jahar Kaduna na cikin jihohin Najeriya da ke da kabilu da mabiya addinai daban-daban kuma a baya an sha samun rikicin kabilanci da addini a jahar saboda rashin fahimtar juna.

A cikin wadannan ranaku na makon fahimtar juna, manyan malaman addinin Kirista sun kai ziyarar karrama Abubakar Ibrahim, wani matashin da ya rubuta Al-qur’ani da ka.

Pastor Yohanna Buru shine ya jagoranci malaman addinin Kiristan zuwa wannan tsangaya.  Ya kuma bayyana cewa, girmama matasan da su ka yi bajinta zai taimaka wajen jawo hankalin sauran matasa don gujewa ayyukan masha’a. Ya ce wannan mako na fahimtar juna zai kara dunkule kan al’umma don kawo cigaban kasa.

A nashi bayanin, Alaramma Ibrahim  mahaifin matashi  Abubakar Ibrahim wanda ya rubuta Al-qur’ani da kaya ce ziyarar malaman Kiristan za ta kara karfafa zumunci tsakanin Kirista da Musulmi.

A hirar shi da Muryar Amurka, Matashin   ya yi bayanin yadda ya samu wannan baiwa ta rubuta Al-qur’ani ba tare da dubawa ba. Ya ce tun yana yaro ya fara nuna shi’awar rubuta Al-qur’ani kuma mahaifin shi ne ya kara karfafa shi.

Makon fahimtar juna tsakanin mabanbanta addinai da kabilu dai kan fara ne duk ranar 13 ga watan Nuwamba kuma ya kare ranar 16 kuma ana sa ran irin wannan ziyarar malaman addinai za ta iya bunkasa fahimtar juna tsakanin al’umomi mabanbanta.

https://youtu.be/wm-2K_nw0vE

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button