News

BIDIYO: Direba ya rasu yayin da jirgin ƙasa daga Legas zuwa Kano ya jirgice a Kaduna

Direba ya rasu yayin da jirgin ƙasa daga Legas zuwa Kano ya jirgice a Kaduna

Jirgin ƙasa mai barin siririn layin dogo da ya taso daga Legas zuwa Kano ya jirgice a Farin Ruwa da ke kusa da Jaji a Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, inda hakan ya yi sanadiyar rasuwar direban jirgin.

Abdullahi Alhaji, Jami’in hulda da Jama’a na Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen Ƙasa ta Ƙasa, NRC, reshen Arewacin Najeriya a Zariya, ya tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN afkuwar lamarin a yau Alhamis a Zariya.

A cewar Alhaji, Bala Kawu, direban jirgin ya rasu ne a yayin da jirgin da ke jigilar kayan lemon kwalba zuwa Kano ya jirgice.

Ya ce lamarin ya faru ne sakamakon lalata ta’annati da a ke yi wa layin dogo a yankin.

Alhaji ya ce a halin yanzu ana ci gaba da aikin fito da gawar direban da kuma tayar da jirgin ya ci gaba da tafiya.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button