BIDIYO: Dalilin Da Yasa Na Ajiye Makamai Na Tare Da Rungumar Sulhu Da Gwamnati- Bello Turji
Gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta bayyana cewa, ba za ta tabbatar da gaskiyar tubar kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ba, har sai ya fito ya ajiye makamansa a bainal jama’a.
A ranar Asabar da ta gabata ne, mataimakin gwamnan jihar ya sanar cewa, Turji ya rungumi shirin tattaunawar zaman lafiya, sannan ya yi alwashin fara kadddamar da farmaki kan sauran ‘yan bindiga a yankin Shinkafi da ke jihar.
A baya dai, gwamnan jihar Bello Matawalle ya bulllo da wani shirin tattaunawar zaman lafiya da ‘yan bindigar a matsayin hanya daya tilo ta kawo karshen hare-harensu da suka dauki tsawon shekaru 10 suna kaddamar wa al’umma tare da sace shanu baya ga garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
An dai samu wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan bindiga da suka mika kansu ga hukuma kamar irinsu Auwalun Daudawa wanda ya kitsa sace daliban makarantar Kankara da ke jihar Katsina a cikin watan Disamban 2020, inda har ya ajiye makamansa a bainal jama’a.
Gadai Cikakken Bidiyon Tare Da Cikakken Bayani Dangane Da Batun
https://youtu.be/nWzdFLhv0l0