Da Na Daina Fadin Gaskiya A Matsayin Liman Gara Na Koma Dako ~ Sheikh Nuru Khalid
Sheikh Nuru Khalid ya mayar da martani kan dakatar da shi daga limanci da kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ƴan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja ya yi masa a masallacin sakamakon hudubarsa ta ranar Juma’a da ta tayar da ƙura a Najeriya.
A hirarsa da BBC malamin ya ce gaskiya ce ya fada a hudubarsa ta Juma’a kuma bai yi nadama ba.
“Idan suka ce na daina faɗin gaskiya a Najeriya, na daina cewa a daina kashe mutane, to gara na yi dako ya fi mun limanci,” in ji Shiekh Nuru Khalid.
Kwamitin Masallacin ƙarƙashin jagorancin Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau ya ce ya dakatar da malamin ne daga Limanci saboda hudubarsa ta tunzura jama’a.
“An ɗauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma’a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai ‘yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi.”
Amma a martaninsa Sheikh Nuru Khalid ya ce ya yi mamakin da mutumin da ya fito daga Zamfara jihar da har yanzu babu zaman lafiya zai fito ya ce ya dakatar da shi saboda ya yi wa’azi kan hana kashe al’umma.
A cewarsa, kashe kashe bai zama tunzura jama’a ba sai don ya ce talaka ya yi hakuri ya zauna lafiya kada ya fito zaɓe sai an daina kashe rayukan mutane.