INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN
Birki Ya Tsinkewa Yaran Hausawa A Social Media, Domin An Samu Wadda Ta Fi Su Ado Gwanja Da Safara’u Yin Wakar Badala
Daga Mahmud Isa Yola
A karkashin wannan rubutu bidiyo ne da ke dauke da yarinya, sanye da himar tana waka. Ga wani sashi da zan iya ambata a rubutu na “cire mata wando kai gaye. Cire mishi wando ke yarinya”. A cikin bidiyon zaku ga yarinya ce, musulma, a zahirance kuma bahaushiya ta ke yin wakar a studio.
A zahirin gaskiya birki ya tsinkewa matasa hausawa, musamman ma mata. Abunda yake faruwa shine: mawaka wadanda babu ruwan su da addini ko al’ada, suna shiga studio suyi wakokin batsa da yaren hausa su sake su a social media. Daga nan sai kaga matasa Hausawa suna hawa kan wakokin suna yin bidiyo suna rawa tamkar sune suke da mallakin wakar, su yi rawar da zata dace da maganar banzan da ake yi a wakar, sannan su sake shi a Tiktok.
Yanzu fitsarar bata tsaya a Tiktok ba, saboda kamfanin Facebook ta kawo irin wannan tsari na kananan bidiyo a Facebook da Instagram wanda yanzu duk inda ka shiga baka tsira da ganin irin wadannan bidiyoyin banzan ba.
Yau nake jin labarin cewa wani lauya ya kai kararar wani mawaki Ado Gwanja, wanda yayi waka yana cewa “baya na yana mini ciwo, asosa chass”. Lauyan ya kalubalanci mawakin inda ya nemi gwamnati ta dau mataki, saboda a cewar sa, tuni mata suka fara rawa da bayan su suna cewa a sosa musu. Haka ma naji cewa (banda tabbaci) hukumar tace fina finai, tana neman wata mawakiyar ita ma (bahaushiya) wacce kwanaki bidiyon tsiraicin ta yayi ta yawo a social media, saboda waken banza da take yi da raye-raye.
Abunda yasa nace birki ya tsinke shine matsalar ba ta bangare daya bane. Mawakan da suke wakokin banza da hausa yanzu sai karuwa suke yi, kuma galibin su matasa ne. Haka kuma yaran hausawa musamman mata sun bude account a tiktok kullum suna jiran a sake musu waka su hau suna rawa. Saboda haka abun ‘supply’ ne ya ci karo da demand. Yaran mata da suke secondary kadan ne basa Tiktok (dalili na saboda na shiga tiktok na gan su dayawa). Suna yin wakokin a makarantun su na islmaiya, zaka ga kawai ta koma gefe tana rawan wakan batsa, da himar din ta, da kayan karatu. Haka ma makarantun boko.
Babu shakka akwai babban aiki, wannan yasa na fitar da shawarwari kamar haka:
1. Gwamnati: A garuruwar da dokokin su basu yadda da irin wadannan ba kamar Kano, wanda da dama daga cikin waken nan daga wurin suke fitowa, wajibi ne gwamnati ta tashi tsaye ta dakile wannan cin fuska wa addini da tozarta al’adan mu na malam bahaushe.
2. Malamai: babu shakka malamai na gargadi akan wannan fitina da ya ratso al’umma, amman dole ne su fahimci cewa fa fitinar ta riga tayi tasiri, watakila har cikin gidajen su ma idan da zasu bincika wayar yaran su. Saboda haka, a babin shawara, yakamata a tsananta gargadi kan mai uwa da wabi.
3. Hukumar Tace fina-finai ta kano: na taba haduwa da Alh. Afakallah a Kano, wurin wani taro inda muka tattauna. Ina fatan har yanzu shine a wurin saboda daga tattaunawa ta da shi nasan mutum ne da yasan aikin sa. Ina kira na musamman a gare shi, ya tashi tsaye, ya hada kai da hukumar hisba wajen yakar wannan musiba wacce tafi tasiri a jihar sa ta Kano.
4. Ina kira ga matasa: mu duba da kyau, duk abunda muke yi, tarihi ne muke bari. In munyi mai kyau, shi zai bi mu a baya. In mun munana kuma haka mummuna zai bi mu. Al’adun mu sun dace da addinin mu, wannan yasa sabawa al’adun hausawa yawanci yana kai ga sabawa addini. Bahaushe mutum ne mai alkunya, ba mutum ne da zai kwaikwayi aladun fasikanci ba. Kuma idan Allah ya mana tsawon rayuwa zamu hayayyafa. Shin ya zaki ji idan watarana kina zaune yar ki ta dauko bidiyon ki kina rawa kina kada bayan ki kina cewa a cire miki wando?
Allah shiryar damu.
Mahmud Isa Yola
[email protected]