BIDIYO: Adam A. Zango Ya Bayyana Yadda Gwamnatin Bazoum Ta Basu Sefa, Miliyan ɗari da tamanin 180
Ba ƙaramin wasa aka yi da kuɗi ba, lokacin PNDS Tarayya ba.
Adam A zango da kansa a cikin wata sabuwar fira, da shi, ya ce; da su ka je, yaƙin neman zaɓe a Nijer Abinda aka ba su kuɗi Sefa, Miliyan ɗari da tamanin 180.
Bayan ƙorafin da yake nuna su Rarara ba su masa adalci ba.
Waɗannan mawaƙan fa da ake gayyatowa daga waje su ne, ƴan siyasarmu ke ɗauka da muhimmanci fiye da matasan ƙasarsu.
A lokacin da miliyoyin matasanmu sun warwatsu Duniya, ba su iya zama kasarsu saboda rashin aikin yi, ko rashin jin daɗin zama, wasu har zuwa bara, Suna ƙasƙanta ƙasarmu. A lokacin fa su ke gayyato mawaƙa suna zuba musu waɗannan maƙudan kuɗaɗe don su yi musu yaƙin neman zaɓe a zaɓe su.
Tabbas wani lokacin ƴan siyasarmu, su ne matsalarmu. Allah ya kyauta.
Ga Bidiyon Ku Kalla Anan