Religion

BIDIYO: Banida Burin Daya Wuce In Samu Mijin Aure Na Gari, Cewar Wacce Ta Lashe Gasar Karatun Alkur’ani Na Kasa

Banida Burin Daya Wuce In Samu Mijin Aure Na Gari, Cewar Wacce Ta Lashe Gasar Karatun Alkur’ani Na Kasa

Ɗan Borno da ƴar Zamfara ne su ka lashe musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa

Abba Goni-Mukhtar, ɗan Jihar Borno da Haulatu Aminu da ga Zamfara ne su ka zamo zakaru a musabaƙar Alƙur’ani mai girma ta ƙasa, karo na 36 da a ka yi a Jihar Bauchi.

Mukhtar da Haulatu sun samu nasarar ne a karatun izu 60, inda shi ya zama zakara a ɓangaren maza, ita kuma a ɓangaren mata.

Sun samu kyautar Naira Miliyan uku-uku da ga Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, inda Musa Ahmed da Fatima Tijjani su ka samu Naira Miliyan biyu-biyu sakamakon karanta izun69 da tajwid da tafsir..

Gwamnan ya kuma baiwa sauran ƴan takarar da wadanda su ka samu nasara da kuma alkalan gasar bisa yadda su ka tsara gasar.

Hakazalika gwamna Mohammed ya bada tallafi karatu ga ƴar shekara 13, Summayya Bauchi, wacce ta wakilci Bauchi s gasar, inda ya bata tallafi karatun sakamakon karanta Alkur’ani daidai-wa-daida.

Ga Bidiyon Nan Ku Kalla, Ubangiji Allah Ya Bata Miji Nagari Amin

https://youtu.be/fbK2Q_74ZkM

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button