Ba ni da Karfin da Zan Yaƙi Gwamnati- Sunday Igboho
mai fafutukar neman ’yancin Yarbawa, Sunday Adeyemo (wanda ake wa laqabi da Sunday Igboho)
ya ce ba shi da Karfin yakar Gwamnatin Tarayya ko Da Kuwa Shugaban Karamar Hukumar mulki.
Sai dai kuma, Sunday Igboho ya ce Allah ne zai yi yakin neman ballewar kabilar Yarbawa.
Dan asalin jihar Oyo ya fadi haka ne a wani bidiyo, inda aka ganshi yana jawabi ga wasu mabiyansa.
A cikin bidiyon, Sunday Igboho ya sake nanata cewa taron da aka shirya na Yarbawa za su zo a Legas a ranar 3 ga watan Yuli, a cewarsa, babu wanda ya fito ya hana shi da mabiyansa kutsawa Legas don taron, yana mai cewa “duk wanda ba zai ba mu dama ba su zo Legas su yi bidiyo ”.
Igboho ya kara da cewa ‘yan Lagos a shirye suke don taron domin sun san zai kasance cikin lumana kamar wadanda aka yi a Ondo, Ekiti, Osun da sauran Jihohin Yarbawa.
Jaridar Lagos Reporters ta rahoto cewa mai fafutukar ya bayyana cewa mutanen da ke wajen kasar suna ta daukar nauyin aikin, yana mai jaddada cewa shi kadai ba zai iya cimma komai ba. “Wadanda ke kasashen waje su ne suke ba da gudummawar kudaden da muke amfani da su wajen sayen motoci da yin wasu abubuwa. Nawa zan iya yi? Sunday Igboho ba shi kadai ne mai iko ba.
Akwai mutane masu iko da yawa a ko’ina, sai dai idan muna so mu yaudari kanmu. Ba zan iya yin shi duka ni kadai ba. Dole ne dukkanmu mu hada kai.
Amma dole ne wani ya fara jagoranci. An zaɓi Musa ne don ya yi wa Isra’ilawa aiki kafin wasu su bi shi. Allah zaiyi mana fada. “Ba ni da ikon fada da Gwamnatin Tarayya. A hakikanin gaskiya, ba zan iya fada da Shugaban Karamar Hukumar talakawa ba. Amma yakin na Ubangiji ne. Allah wanda shine shugaban yakin zai yi yaki domin mu.
Zamaninmu zai ‘yantar da ƙabilar Yarbawa daga bautar. “Ga dukkan Yarbawa, ku fito ranar 3 ga Yuli don gangamin lumana. Bai kamata mu yi faɗa ba. Muna so kawai mu gaya wa Buhari cewa duk abin da muke so shi ne al’ummar Yarbawa. Babu wanda ya isa ya yi mana barazanar mutuwa. Ba za ku iya kashe mu ba. Babu zakara kai tsaye, amma zakaran yanzu, ”in ji Igboho