Religion

BABBAR MAGANA: Nabar Addinin Musulunci Na Koma Addinin Budda ~ Cewar Muneerat Abdulsalam

BABBAR MAGANA: Nabar Addinin Musulunci Na Koma Addinin Budda ~ Cewar Muneerat Abdulsalam.

Shahararren mai kalaman batsa a shafukan sada zumunta Wato Muneera Abdulsalam ta bayyana cewa ta bar addinin musulunci ta koma addinin Budda.

Muneera wadda ta baiyana hana a shafinta na sada zumunta, ta ce a baya ita Kirista ce, amman daga baya ta dawo addinin musulunci.

A yanzu kuma ta chanza shawara tare ta yanke shawarar komawa addinin Budda saaboda wasu dalilai na kashin kai.

Yanzu dai Muneera ta ce ita yar addinin Budda ce ba musulma ba. Domin wasu musulman na kyamar sana’arta ta batsa a shafukan sada zumunta.

Muneerat dai tasha janyowa kanta abubuwan magana a shafukan sada zumunta, wanda wasu ke ganin tana yin hakan ne da nufin kara samun mabiya a dandalin sada zumunta.

Domin da yawan mabiyan da take samu ne, take kara samun masu kallon batutuwan batsan da take wallafawa a dandalin sada zumuntan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button