ANNABI BA WASA BA: Lauyar Da Tayi Bayani Kan Dokar “Defense of Provocation” Don Kare Masoya Manzo Allah S.A.W A Sokoto Ta Samu Lambar yabo
Daga Muryoyi
An samu mace lauya ta farko daga yankin Arewa Hausa – Fulani da ta samu shiga cikin jerin fitattun matasa 100 da ake karramawa duk shekara a masarautar Ooni da sukayi fice a fannin kyautata jin dadin rayuwar jama’a a fannoni daban-daban na rayuwa kama daga fasaha, kimiyya da kirkire-kirkire, sana’o’i da sauransu.
Wannan hazikar mace kuwa itace matashiyar lauyar nan da tayi suna a fagen jin kai, wacce aka dade ana damawa da ita a fannin kare yancin mata da yara, Barrister Aysha Ahmad.
Babban Basaraken Kudu “Ooni of Ife”, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II, ya karrama Barrisater Aysha Ahmad da lambar yabo a bikin Royal African Young Leadership Forum (RAYLF) Award.,
Ayasha wacce a yanzu haka take rike da Daraktan sashen shara’a na hukumar tara kudaden haraji na Kaduna (KADIRS), ta shahara wajen taimakon jama’a da kare hakkin ‘ya’ya mata.
Ta sha samun lambobin yabo da karramawa a lokuta daban-daban a fagen aikinta.
Ko a yan kwanakin nan Barrister Aysha ta samu yabo da addu’oin Alkhairi sosai biyo bayan yadda ta tsaya tsayin daka wajen kare martabar Manzon Allah S.A.W ba tare da shakka ko shayin kowa ba a lokacinda ake tsaka da cece-kuce kan abunda ya faru a Sokoto.
Ooni yace An zabo Aysha ne sakamakon ficen da tayi wajen taimakon al’umma, kwarewar ta wajen aiki, da salon iya jagoranci, da tausayin ya’ya mata da bi masu hakkinsu, kana uwa uba da jajircewar ta da kuma rashin tsoro.
Barrister Aysha ta karbi kambun karramawar ne a dakin taro na Oduduwa Hall dake Obafemi Awolowo University, a ile-Ife.
Rashin tsoro da sanin makamar aiki yasa Barrista Aysha ta fita tayi bayani akan “Defense of Provocation” wanda ya dauki hankalin duniya musamman malaman addini da masoya manzon Allah SAW
Wane fata zaku yi mata?