News

Amurka Za Ta Tallafawa Najeriya Da $55m Cikin Gaggawa Don Shawo Kan Tsada Da ƙarancin Abinci

Amurka Za Ta Tallafawa Najeriya Da $55m Cikin Gaggawa Don Shawo Kan Tsada Da ƙarancin Abinci

Amurka ta sanar da shirin tallafawa Najeriya cikin gaggawa da dala miliyan 55 domin taimaka wa ƙasar wajen shawo kan matsalar tsada da ƙarancin abinci.

Wannan wani ɓangaren ne na alkawarin Shugaba Joe Biden a taron G7 da aka gudanar a Jamus, a ƙoƙarin ceto ko kare matalautan ƙasashen daga matsalar abinci da ke addabar duniya sakamakon mamayar Rasha a Ukraine.

Amurka ta sanar da wannan shiri ne a wata sanarwa da ofishin jakadancinta a Najeriya ya fitar, inda take cewa waɗannan kuɗaɗe za a bayar da su ne ta hannun Hukumar raya ƙasashe ta Amurka, wato USAID ƙarƙashin shirinta na noma, ciyarwa da taimakon agaji.

Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, a cikin sanarwar tana cewa kuɗaɗen za su taimaka wajen shawo kan matsalolin tattalin arziki, wadatuwar abinci da abinci mai gini jiki a yankunan da mutane ke fama da talauci a Najeriya, da kuma tsadar rayuwa da ke sake taggayara al‘ummarta.

Mary Beth Leonard, ta kuma sake jaddada munufofin Amurka da al’ummarta domin inganta tattalin arzikin ɗaiɗaikun mutane da sama musu abinci wadatacce a Najeriya.

Ta ce Amurka za ta ci gaba da tallafa wa wanzuwar tattalin arzikin Najeriya, kuma ƙasar za ta cigaba da mutunta daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakaninta da gwamnatin Najeriya, kamfanoni da ƙungiyoyi masu zaman kansu wajen shawo kan matsalolin ci gaba da jin-ƙai cikin gaggawa.

Ta kuma jajantawa ƴan Najeriya kan wahalhalun da suka tsinci kai sakamakon mamayar Rasha a Ukraine da suka haddasa tsadar kayan abinci.

Amurka dai na cewa wannan taimako da Shugaba Biden ya gabatar zai taimaka wajen ceto Najeriya daga tasku da matsalolin tattalin arzikinta suka jefa ta.

Tun soma yaƙin Ukraine, Amurka ke tallafa wa ƙasashen duniya da kuɗaɗen da yawansu ya kai dala biliyan 5.6, domin shawo kan matsalolin ƙarancin abinci da tsadar rayuwa.

Najeriya, kamar sauran ƙasashen duniya na cikin yanayi mai tsanani da hauhawar farashi, yanayin da ya ƙara wa mutane talauci da tursasawa iyalai da dama faɗawa cikin yanayi na uƙuba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button