Amarya Ta Rasu Ana Saura Sati Biyu A Daura Aurenta Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un
Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu-yanzu Na Cewa, Wata Budurwa Ta Rasu Saura Ana Saura Sati Biyu A Daura Aurenta.
Kamar Yadda Muka Samu Wannan Rahoto Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto Wanda Aka Wallafa A Shafin Rariya.
Allah ya yi wa wannan yarinyar mai suna Aisha S Gobir rasuwa a sanadiyar haɗarin motar ya faru da ita da yayarta a hanyarsu ta zuwa Birnin Kebbi wajen ziyarar ‘yan uwansu.
Tuni ita yayarta ta rasu bayan haɗarin, sannan daga bisani ita ma Ƙanwarta Aisha S Gobir Allah ya ɗauke rayuwarta a jiya.
Allah ya jikansu da rahamarsa yasa Aljannah ce makomarsu.