ALHAMDULILLAH: Sanatocin Arewa sun nuna rashin goyon bayan su kan amfani da karfin soja don kwato mulkin kasar Nijar.
Majalisar Sanatocin Arewa na Majalisar Dattawa ta 10 karkashin jagorancin Sen. Abdul Ahmad Ningi, sunyi Allah wadai da yin juyin mulki da sojojin kasar Nijar suka yi. Sanatocin sun bayyana rashin goyon bayan su na amfani da karfin soja kamar yadda ECOWAS take kokarin yi.
Sanatocin sunce ya kamata ECOWAS ta maida hankali kan hanyoyin siyasa da diflomasiyya don maido da mulkin dimokradiyya a Jamhuriyar Nijar cikin zaman lafiya. Sunce idan har aka yi amfani da makami tabbatas talakawan yankin Arewa da al-ummar Nijar da ba suji ba, basu sani zai shafe su, za su shiga cikin mayuwancin hali.
Sanatocin sun bayyana matsayar su ta hannun kakakin su Sanatan Kano ta kudu Sen. S A Kawu Sumaila, OFR Ph.D.
Hakika naji dadin wannan nuna kishin da Sanatotinmu suka yi, saboda duk wani mai hankali yasan da wannan rikicin ya shafi Arewa ne kai tsaye.
Muna Addu’ar Allah yasa a shawo kan matsalar ba tare da tashin hankali ba.
✍️ Comr Abba Sani Pantami