An Sace Yarinya Mai Shekaru 5 Tare Da Yin Garkuwa A Jihar Kano.
Wasu masu garkuwa da mutane sun sace wata yarinya mai shekara biyar a birnin Kano ranar Asabar, a cewar rahoton jaridar Dailynigerian.com
Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a unguwar Kawaji bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku ko kuma Adaidaita-Sahu.
Wani kawun Hanifa ya shaida wa jaridar cewa mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.
BbcHausa.com ta yi yunƙurin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Kano amma mai magana da yawunta ya ce yana cikin wata ganawa.
“Babu nisa tsakanin makarantar da gidansu (Hanifa), saboda haka yaran sun saba zuwa da ƙafarsu,” a cewar Suraj Zubair.
“Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce ɓarayin sun zo ne a Adaidaita-Sahu kuma suka ce za su kai su gida. Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita.”
Birnin Kano ya sha fuskantar sace-sacen ƙananan yara a ‘yan shekarun nan, abin da ya sa Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa kwamatin bincike domin ganowa da kuma bin haƙƙin yaran da ake sacewa.
A Oktoban 2019, rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wasu da ake zargin sacewa da kuma safarar yara ‘yan asalin jihar zuwa garin Onitsha na Jihar Anambra da ke kudancin ƙasar, inda ake tilasta musu sauya addini da al’ada.