Manyan Dalilan Da Yasa Farfesa Ibrahim Maqari Ya Janye Karar Da Ya Shigar Kan Abdullahi Gadon Kaya
Malamin addinin Islama, Kuma limamin Babban masallacin kasa dake birnin tarayya, Abuja, Wato Farfesa Ibrahim Makari, Ya bayyana janye karar da ya shigar kan Dr Abdallah Gadon Kaya dake jihar Kano kan zargin ya bata masa suna.
Malamin ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da Arewa News Eye ta samo a yayin wani karatu da yake gabatarwa, inda ya bayyana dalla-dalla dalilan da yasa ya janye karar.
Idan zaku iya tunawa, Makari ya shigar da kara ne, inda ya nemi kotu ta bi kadunsa bisa wasu maganganu da Gadon Kaya ya furta akansa, wadanda Makari ya dangantasu da bata suna.
Farfesa Ibrahim Makari ya janye karar da ya shigar kan Dr Abdallah Gadon Kaya a kwanakin nan A baya Farfesa ya maka Dr a kotu ne bisa zarginsa da bata masa suna tare da fadin maganganu akansa Farfesa a wani bidiyo da muka samo ya bayyana dalilai da suka sanya ya janye karar da a shigar.
Idan zaku iya tunawa, Makari ya shigar da kara ne, inda ya nemi kotu ta bi kadunsa bisa wasu maganganu da Gadon Kaya ya furta akansa, wadanda Makari ya dangantasu da bata suna.
Manyan Najeriya ne suka sanya ni janye karar Bayan da aka kai takardar kara ga Dr Gadon Kaya, malamin ya ce wasu manya a Najeriya, kuma masu fada a ji sun jawo hankalinsa, kuma sun nemi lallai ya janye karar.
A cewarsa: “Manya a kasar nan, sun shigo sun nemi a bar musu shari’ar. Ma’ana su za su yi shari’ar kar aje kotu.
Kuma cikinsu akwai shugaban hukumar tsaro na kasa gaba daya, da wasu.
Na fada musu cewar zan sanar sunce ba laifi in sanar… “Kuma abin ya shafi har iyaye har da mahaifina duk sun amince a kan hakan, sun zabi hakan. Saboda haka, dalilin haka sun ce su a barsu za su nemi wannan mutumin da yayi maganganu ya fito da hujjar da yace yana dashi su ya basu hujjar.
“Idan bai da hujja za su nemi ya rubuta a rubuce cewar ba shi da hujja.” Makari ya jaddada hakan da cewa, ya amince da bukatarsu kasancewarsu iyaye, kuma masu fada a ji ba wai a kansa kadai ba, a kasa baki daya.