Trending

Gwamnatin Nigeria Ta Haramta Hada Hadar Kasuwancin Crypto currency exchange A Kasar Baki Complete 1

Gwamnatin Nigeria Ta Haramta Hada Hadar Kasuwancin Crypto currency exchange A Kasar Baki Daya Complete 1

Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar hana kamfanin kirifto na Binance da sauran kamfanonin hada-hadar kuɗaɗen intanet yin hada-hada da kuɗin ƙasar, domin dakatar da abin da ta kira ‘yawaitar’ tashin farashin kuɗin ƙasar waje.

Da dama daga cikin ‘yan ƙasar na zargin cewa masu hada-hadar kuɗin kan duba shafin Binance da ake sabunta bayanai a kowace rana domin sanin farashin da za sayar da kudin kasar wajen.

Wannan na zuwa ne sakamakon tashin gwauron zabi da farashin kuɗin ƙasar waje ke yi a Najeriya, inda wasu ke zargin kamfanin Binance da sauran kamfanonin kuɗin intanet da yin uwa da makarɓiya wajen saka farashin dalar.

Yawaitar faraduwar darajar kuɗin Najeriya a baya-bayan nan na ci gaba da haddasa fargaba a zukatan ‘yan ƙasar, inda farashin kayayyaki ke cigaba tashin gawauron zabo, lamarin da ya jefa ‘yan kasar da dama cikin mawuyacin hali.
A ranar Labara dai an sayar da dala kan 1,800 a kasuwannin bayan fage.

A kokarinta magance matsalar gwamnatin ƙasar cikin watan Yulin 2023, fito da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen daidata kasuwa hada-hadar kuɗaɗen wajen.

Read More

Gwamnatin Najeriya dai ta sha cewa tana ɗaukar matakan da suka dace don magance karyewar darajar kuɗin ƙasar.

Forex
Forex

Sannan a watan Agustan 2023, babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL ya karɓo bashin dala biliyan uku daga bankin Afrexim da zai biya da man fetur, domin tallafa wa gwamnatin ƙasar wajen daidaita farashin naira a ƙoƙarinta na cimma burin gwamnati.

Haka ma a watan Janairun 2024, babban bankin ƙasar, CBN ya ware kusan dala miliyan 61.64 domin warware bashin da kamfanonin jiragen waje ke bin ƙasar .

Ga kuma tarin samame da jami’an hukumar EFCC ke kai wa ‘yan kasuwar chanji, duk dai da nufin daidaita farashin kuɗin ƙasar waje a faɗin Najeriya.

To sai dai duk da waɗannan matakai da gwamnatin ƙasar ta dauka da alama kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.

Shi ne yanzu gwamnatin ke tunanin ɗaukar matakan rufe kamfanonin hada-hadar kuɗin kirifto, da nufin magance matsalar.

Gwamnatin ta ce ta samu bayanan cewa masu yaɗa jita-jita da masu almundahanar kuɗi na amfani da kamfanonin wajen aikata laifukansu.

Hukumomin ƙasar sun ce laifukan da ake aikatawa a shafukan kamfanonin kirifton su ke ƙara ta’azzara tashin farashin kuɗin kasar wajen tare da karyewar darajar kuɗin kasar wato naira.
Muhammad Inuwa Aliyu wani masanin hada-hadar kuɗin kirifto a Najeriya ya ce Binace wani dandali ne da ake hada-hadar kuɗin intanet a duniya.

Kamfanin ya kasance ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke hada-hadar kuɗin intanet na duniya.

Masanin ya ce kamfanin Binance shi ne kan gaba wajen hada-hadar kuɗin intanet a duniya idan aka kwatanta da takwarorinsa irin su Bitcoin da sauransu.

Nigeria
Nigeria

Cibiyar kamfanin Binance


Changpeng Zhao ne ya samar da kamfanin ‘Binance Holdings Ltd’ a shekarar 2017.

An kuma fara buɗe kamfanin a ƙasar China, sannan ya koma Japan bayan da gwamnatin China ta ɓullo da matakan takaita ayyukan kamfanonin kirifto a ƙasar.

Sannan daga baya kamfanin ya fice daga Japan inda ya koma ƙasar Malta.

A shekarar 2021, hukumar shari’ar Amurka da hukumar tara kuɗin shiga ta ƙasar suka shigar da ƙarar kamfanin kan zarge-zargen laifukan haraji da halasta kuɗin haram.

Yaya kamfanin ke aiki?

Kamfanin Binance da na wani tsari da masu amfanin da shi ke buɗe asusun ajiyar kuɗin intaten wanda da shi ne ake hada-hadar kuɗaɗen intanet a shafin.

Binance na amfani da kuɗaɗen da ake kira USDT wanda da shi ne ake hada-hadar kuɗin intanet shafin.

Kamfanin ya bai wa kuɗin kowace ƙasa daraja gwargwadon bukatar kuɗin shafin.

A shafin Binance babu iyakar kuɗin da za a iya tura wa mutum, saɓanin yadda tsarin Najeriya yake na dala 10,000 zuwa ƙasar waje, kamar yadda masanin ya yi bayani.
Muhammad Inuwa Aliyu ya ce kamfanin Binance ya amince da hada-hada da kuɗaɗen ƙasashe da dama a shafin, to amma banda kuɗin Najeriya wato naira, a maimakon haka sai dai a sayar da USDT da ke cikin asusun ajiyarka na Binance, sannan a tura maka naira zuwa asusun ajiyarka na banki.

Hakan ya sa matasan Najeriya da dama suka rungumi harkar, saboda hada-hadar da ake yi a Binance ba ta da iyaka.

To kuma kasancewar Najeriya ƙasa ce da ta dogara da shigo da kayyaki daga ƙasashen waje, kuma bankuna sun fara kayyade adadin dalar da za su bai wa ‘yan kasuwar, sai kuka koma amfani da Binance saboda a nan za a ba su adadin kuɗin da suke so domin sayo duka abubuwan da ke suka muradi.

”Yanzu misali in za ka bar Najeriya da dala, iya dala 10,000 kawai za ka iya fita da ita a ƙa’ida, to amma a Binance za ka iya tura wa mutum dala miliyan 100 ma a lokaci guda”, in ji shi.

”Domin kuwa farashin dalar ɗaya yake a yadda yake a CBN da kuma yadda yake a Binance”, in masanin kirifton.

”Idan aka gaya maka ‘yan Najeriya da ke amfanin da Binance a yanzu za ka sha mamaki”, in ji masanin.

Masanin ya ce a yanzu ‘yan Najeriya da dama da ke son ɓoye wasu kuɗin almundana a asusun ajiyarsu na Binance kawai za su tura kuɗin.

Shi kuɗin da ake ajiyewa a Binance kuɗi ne da ba a iya ganinsu, don haka dole idan kana son amfani da su sai dai ka sayar wa wani da ke amfani da Binance, shi kuma ya tura maka naira cikin asusun ajiyarka na banki.

”Yadda ake yi shi ne idan kana da kuɗi a susun ajiyarka na Binance, kuma kana son sayarwa za ka rubuta ne a shafin Binance cewa kana da adadin kuɗi kaza, kuma kana son sayar da su domin karɓar naira, daga nan wanda ke son saya sai ya danna alamar saye a ƙasan rubutun naka, sai shi kuma kamfanin Binance ya ɗauke kuɗin ya riƙe a wajensa, sannan ya tura wa mai sayen asusun ajiyar mai sayarwar, inda shi kuma zai tura masa naira, sannan Binance ɗin ya tura wanda ya saya ɗin USDTn naka”, kamar yadda masanin ya yi bayani.

Masanin ya ce sakamakon yawaitar sayen dala da naira da ake yi a Binance ya sa koyaushe farashin nairar yake kara karyewa.

Kuma shi dama Binance ba ya amfani da farashin gwamnati wajen sayar da dalar, yan sayar da shi ne yadda kasuwar buƙatarsa ta nuna.

”Kasan mu ‘yan Najeriya ba mu iya abu, za ka samu mutum guda ya yi almundahanar kusan dala miliyan guda, sai ya je ya saka a asusunsa na Binance, to saboda yadda ake yawaitar cinikin dala da naira a kamfanin shi yasa kullum dalar take tsada saboda yadda ake yawan cinikinta”, in ji shi.

Yadda za a magance matsalaar

Masanin kirifton ya ce ‘yan Najeriya kimanin miliyan 18 ne ke da asusun ajiya a Binance, don haka a ganinsa abin da ya kamata gwamnatin ƙasar tagayyato kamfanin domin tattauna matakan da ya kamata a bi ta yadda farashin kuɗin ƙasar zai farfaɗo a kamfanin Binance.

In kuma kamfanin ya ƙi amincewa da lalubo hanyoyin warware matsalar da gwamnatin Najeriya to gwamnati ta ce za ta yi ƙarar kamfanin domin ta cire naira a tsarinsa.

”A yau idan aka cire naira a cikin hada-hadar Binance, ina mai tabbatar maka da cewa kamfanin sai ya girgiza, saboda yadda ‘yan Najeriya ke hada-hada a kamfanin”.

visit our Facebook

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button