Kunji Kalaman Ahmad Musa Kan Masu aibata Yan Wasan Super Eagles Nigeria
Ɗanwasan kwallon ƙafa na Najeriya, Ahmed Musa ya yi kira da mutane da su daina zagi da aibata ɗanwasa, Alex Iwobi, a shafukan sada zumunta.
A cewar ɗanwasan tsakiyar, zagin ba kawai keta mutuncin Iwobi ya ke yi ba, hakan wani babban laifi ne.
“Wannan alama ce ta munafurci muna ikirarin cewa kwallon ƙafa na haɗa kanmu amma muna nuna wannan hali.”
Inda ya ƙara da cewa rashin nasarar da ƙungiyar kwallon ƙafar ƙasar ta samu abu ne mai matuƙar ciwo, amma ɗora alhakin hakan kan ɗankwallo guda ɗaya rashin adalci ne.
Ahmed ya bayyana cewa nasara ta su ce gaba ɗaya ƙungiyar, haka kuma rashinta ta shafe su ne gaba ɗaya.
Yana mai kare Iwobi da cewa ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a filin wasa kamar sauran takwarorinsa.
“Maimakon yaɗa abubuwa marasa daɗi, ya kamata mu nuna ƙauna ta haƙiƙa da goyon baya ga ƴanwasanmu, suna buƙatar mu basu kwarin guiwa a yanzu fiye da kowane lokaci…”
Tun bayan kammala gasar kwallon ƙafa zagayen ƙarshe da aka yi tsakanin Ivory Coast da Najeriya, ake ta zagi da aibata Alex Iwobi a kafafen sada zumunta.
Lamarin da ya kai shi ga ƙauracewa shafukansa tare da goge wasu abubuwan da ya wallafa.
Najeriya ta sha kaye a hannun mai masaukin baƙi da ci 2-1 a gasar wasan kwallon ƙafar ta nahiyar Afrika wadda aka kammala a ranar Lahadi.
Visit our Facebook