Politics

Kotu Ta Tabbatar Da Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano da aka yi a watan Maris

Kotu tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano da aka yi a watan Maris

A zaman da kotun ta yi yau a Abuja, ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano da aka yi a watan Maris.

Kotu tace AKY ba dan NNPP bane a lokacin da ya shiga zabe. Saboda haka bai cancanta ya tsaya takara ba. Tribunal tayi kuskure da ta gaza fadar cewa bai cancanta ba tun a farko.

Section 177 of the Constitution requires one to be a member of a political party before he could be vie for an electoral office.

Wajibi sai mutum ya zama dan jam’iyya kafin ya cancanta tsayawa takara Nigeria.

Mulki kayan Ubangiji ne, Idan ya kaddara zamu cigaba ba makawa zamu cigaba zamuyi nasara a Supreme Court.

Idan kuma bai kaddara ba hakan ma da yayi mana mungode masa, Yabamu dama muma muma mukayi.

Rayuwar mu ta baya munyi babu mulkin a hannun mu kuma Allah yayi mana komai, ba lallai saida mulki ake rayuwa ba, Allah duk yanda kayi damu mungode, – A Cewar Shafin Jam’iyyar NNPP

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button