Abduljabbar Yana Kokarin Bijirewa Muqabalar Da Gwamnatin Kano Ta Shirya. Kamar Yadda Shafin Tijjaniya Online Suka Wallafa A Shafin Na Facebook Cewa.
Rahotanni na bayyana yadda Abduljabbar Kabara ke kokarin bijirewa Muqabalar da gwamnatin Kano ke shirin yi ta hanyar yadda Abduljabbar ke kafa wasu sharudda da ka’idoji wadanda ke bayyana tsoronsa a zahiri.
Abduljabbar wanda ya yi ta kira ga gwamnati kan ta samar da wannan muqabala yanzu haka ya ce dole gwamnati ta ba shi dama ya zabi malaman da yake so, sannan shi zai zabi mas’alolin da za a tattauna a kansu.
Wannan ba komai ba ne sai rainin hankali da gazawa. Kai da kullum burinka a fito a yi muqabala da kai an amince za a zauna da kai saboda rashin kunya da fitsara har sai ka zabi wadanda kake so? Wannan ba komai ba ne sai borin kunya da tsoro, dama ai anjima ana nemanka muqabala kana kin amincewa don kar a tona karairayi da ha’ince-ha’incen da kake rudar wawayen da ka tara a gabanka.
Shi Abduljabbar yana tunanin idan ya yi wa gwamnati tahaddin muqabala ba za a amince ba. Yanzu da aka amince ga shi yana kokarin zillewa don kar a tona masa asiri, kamar ba shi ne ke cika baki ba.
Shawarata ga gwamnati shi ne, ta tursasa shi zama muqaba koda ma waye, idan ya ki ta zartar da tsattsauran mataki a kansa.
Malaman da nake ra’ayin su ya kamata su zauna da Abduljabbar a bangaren Tijjaniya akwai Malam Abubakar Madatai dama ya jima yana neman ya zauna da shi yana zillewa. Sai kuma Abulfatahi Attijjany wannan kam tamorawa idan suka ji muryarsa firgicewa suke saboda dukan kawo wuka da yake yi wa Abduljabbar.
A Bangaren Salafiyya Malam Alqasim Hotoro da Malam Kabiru Bashir Abdulhamid tabbas wadannan Malamai sai sun yi masa kamshin mutuwa.
A bangaren Kadiriyya kuma a zabi tsohon dalibinsa Malam Mas’ud Hotoro da kuma dan gidan Khalifa Dr Alfatih Qaribullah wadannan ba zai ji da dadi a wajensu ba. Amma Abduljabbar ya yi tsararo manyan Malamai su zauna da shi a matsayinsa na cikakken dan iskan gari wanda duniya ta tabbatar da yana da matsalar tabin hankali. Mun amince idan ya cinye wadannan da na am