LABARI MAI DADI: Gwamnatin Najeriya za ta dauki sabbin ma’aikatan N-Power, da kuma biyan dukkannin bashikan da masu aikin N-Power din suke binta.
Ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci Dr Betta Edu, ta ce ana shirin yin kwaskwarimar shirin N-Power domin daukar karin mutane da kuma tabbatar da biyan kudaden alawus-alawus din, wadanda suke amfana da shirin cikin gaggawa, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito yanzu.
Ministar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a yau Lahadi, da ta gabatar ta hannun mai ba ta shawara ta musamman kan harkokin yada labarai Rasheed Zubair, a Abuja.
Sanarwar ta ruwaito ministar na cewa nan ba da jimawa ba za a magance kalubalen da masu cin gajiyar N-Power ke fuskanta ta fuskar jinkiri wajen biyan kudaden alawus din su, da kuma daukan sabbin ma’aikatan N-Power din.
Ministar ta kuma ce ma’aikatar ta shirya samar da cibiyoyin jin kai a fadin kananan hukumomi 774 na kasar, inda ta kara da cewa za ta kasance cikin gaggawa wurin kawar da talauci a Najeriya.
✍️ Comr Abba Sani Pantami