Religion

Na Dawo Daga Rakiyar Soyayyar Farfesa Maƙari, Yanzu Ba Irinsa Nakeso Na Aura Ba”. – Zainab

Na Dawo Daga Rakiyar Soyayyar Farfesa Maƙari, Yanzu Ba Irinsa Nakeso Na Aura Ba”. – Zainab

A Yanzu Ba Irin Su Farfesa Ibrahim Maƙari Na Ke Buƙata Na Aura Ba, Cèwar Yar Gwagwarmaya Zainab Naseer Ahmed

Ada Na Kamu Da Soyayyar Farfesa Maƙari, Amma Yanzu Na Dawo Daga Rakiyar Soyayyarsa”. – Zainab

….Ina Buƙatar Na Auri Mutum Ɗan Tsaka-Tsaki, Wanda Shi Ba Yaro Ba Ne Kuma Ba Tsoho Ba Ne, In Ji Ta.

Fitacciyar matashiyar nan mai fafutukar kare haƙƙin mata da yara ƙananan a Jihar Kano, Comrade Zainab Naseer Ahmad ta bayyana cewa ada ta kamu da soyayyar fitaccen malamin addinin musuluncin nan, mai Limanci da karantarwa a birnin Abuja, Shaikh Ibrahim Ahmad Maƙari, amma a yanzu ba ta son sa.

A shekaru biyu baya dai Zainab da kanta ta bayyana a shafinta na Facebook cewa: “jin wani abu na alamar kamuwa da soyayyar wani ba abu ne da ya ke faruwa cikin sauƙi a gare ni ba, hasalima aure ba ya gabana ko kaɗan a halin yanzu, sai dai kuma a yanzun na yi mamaki da na ji na kamu da soyayyar Farfesa Ibrahim Maƙari har ma na ji ina so na aure shi”. In ji ta.

A tattaunawar da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta yi da ita a wannan lokaci, Zainab ta bayyana cewa tabbas shekaru biyu da su ka wuce ta kamu da tsananin soyayyar Farfesa Maƙari amma a yanzu ya fita a ranta, ta daina son sa.

“A yanzu na ji ba na son Shaikh Maƙari saboda na lura ba ya cikin irin mazan da na ke so na aura. A yanzu ina so ne na auri namiji ɗan sumul-sumul ne wanda shi ba yaro ba ne, kuma ba tsoho ba ne. Mutum dai irin tsaka-tsakin nan, shi na ke so na aura a yanzu”. In ji ƴar gwagwarmaya, Zainab Naseer Ahmed.

Zainab dai ta yi ƙaurin suna wajen fito da maganganu masu tada hazo a Social Media. Ta taɓa cewa babban burinta a rayuwa shi ne ta ga ta zama shugabar ƙasa ko gwamnar Jihar Kano, kuma ita ce ta taɓa cewa yin aure ba wata nasara ba ce da ɗan adam zai yi alfahari da cewa ya cimma wani buri ba, maganganun da su ka mamaye sabbin kafafen sadarwa na zamani aka yi ta tafka muhawara a kansu.

Mè zakù cè?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button