SUBHANALLAHI: Bayan Gabatar Da Ƙona Alƙur’ani A Kasar Sweden, Salwan Momika yayi alƙawarin kara ƙona alƙur’ani mai girma
Makiyin musulunci Salwan Mika, haifaffen kasar Iraq shine ya ƙona Alƙur’ani mai girma a wajen babban masallacin Stockolm wato babban birnin kasar Sweden.
Kone Alƙur’anin ya faru ne yayin da yayin da musulmai ke bikin Idin Babbar Sallah a ranar larabar da ta gabata.
Momika ya bayyana alƙur’ani a matsayin littafin dake tauye hakki da Dimokuraɗiyya.
Sai dai da yawa yan kasar Sweden basu yarda da matakin ba, har ta kai wasu sunyi zanga-zanga tare da bayyana abinda momika yai a matsayin tada zaune tsaye.
Dukda rashin amincewa da matakin Silwan Momika ya kuma yi alkawarin kara ƙona alƙur’ani mai girma a nan gaba