Tirqashi: Lallai Abba Kabir Yusif Dagaske Yake Bada Wasa Yazo, Ya Bukaci Gidajen Su Sayar Da Mai A Tsohon Farashi.
Sabon Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci dillalan man fetur da su ci gaba da sayar da man kan farashin da aka saba domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta a halin yanzu.
Gwamnan ya ce yana sane da cewa har yanzu dillalan na da ragowar man da ya kamata a ce sun sayar a kan tsohon farashi.
Cikin sanarwar da Sakataren yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya ce idan ana son rage wahalhalun ‘yan jihar, ya kamata dillalan su yi hakuri su sake bude duk gidajen mai da ke da man fetur a kasa su kuma sayar a kan tsohon farashi.
“A matsayina na gwamna, na ji takaicin ganin yadda al’ummar Kano ke shan wahala sakamakon kara farashin man fetur da ba gaira ba dalili, kuma dole a kawo karshen lamarin nan take,” a cewar gwamnan.
Ya kara da cewa Kano ita ce cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya har ma da wasu kasashen Afirka ta yamma kuma al’ummarta na cigaba da morewa yanayin kasuwanci mai kyau.
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar Kano da su ci gaba da bin doka domin gwamnati a ko da yaushe a shirye take ta tabbatar da cewa mutane suna gudanar da harkokinsu cikin sauki.