News

Masha Allah: Ansamu Nasarar Kwashe Daliban Nigeria Da Suka Makale A sudan

Hukumar lura da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje NIDCOM ta ce zuwa yanzu, an yi jigilar an Najeriya 2,246 daga Sudan mai fama da yaƙi.

Shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar, Abdurrahman Balogun ne ya bayyana hakan yau Juma’a lokacin da yake bayar da ƙarin haske kan ƙoƙarin da gwamnatin Najeriya ke yi na kwashe jama’arta da suka maƙale a rikicin na Sudan.

Balogun ya ƙara da cewa a ranar 5 ga watan Mayu, ƴan Najeriya 130 ne suka biyo jirgin Tarco sai kuma ranar 6 ga watan na Mayu, aka samu mutum 131 da suka biyo jirgin daga Port Sudan. Akwai kuma mutane 102 da suka iso Najeriya ranar Lahadi daga Port Sudan ta jirgin na Tarco.

Ya ce a ranar 3 ga watan Mayu, an kwaso mutum 94 – maza 78 sai mata 16 a jirgin sojin sama ƙirar C130 yayin da mutum 374 kuma suka isa Najeriya a jirgin kamfanin Air Peace.

A jawabin nasa ya ƙara da cewa wasu ƴan ƙasar 410 cikin jirgin Max Air sai wasu 322 a Azman da suka taho daga filin jirgin sama na Aswan ranar Lahadi.

Balogun ya bayyana cewa jirage biyu daga kamfanin Tarco sun kwashe ƴan Najeriya 133 ɗauke da yara 7 da jarirai tara, sannan wani kashin fasinjoji 126 tare da yara 12 da jarirai 41 da suka isa Najeriya daga Port Sudan ranar Litinin da Talata.

Ya kuma ce ƴan Najeriya 123 sun bi jirgin Tarco a ranar Laraba daga Port Sudan yayin da wasu 136 kuma suka isa Najeriya a ranar Alhamis.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button