Tirqashi: An Kai ƙarar Mawaƙi Rarara Wajen Sarkin Katsina Da Sarkin Daura
Lauyoyi a Kano sun kai ƙarar mawaƙi Rarara wajen Sarkin Katsina da Sarkin Daura.
Wasu lauyoyi masu zaman kansu dake Kano sun kai ƙarar mawaƙi Dauda Kahutu Rarara wajen Sarkin Katsina da Sarkin Daura bisa zargin da akeyi masa na cin zarafin wasu shuwagabannin jihar Kano da yayi a cikin waƙokin sa.
Lauyoyin sun roƙi Sarakunan da su tsawatar mashi domin ya tuba kuma ya janye kalaman sa akan shuwagabannin tare da neman yafiyar su don a zauna lafiya.
Barrister Badamasi Sulaiman Gandu, wani lauya mai zaman kansa a jihar Kano ne ya bayyana haka a cikin wata fira da yayi a Freedom Radio.
Barrister Gandu ya bayyana cewa tun da farko sun tura ma mawaƙin wasiƙa dake ɗauke da jan hankali da kira agareshi da ya tsaftace siyasar shi da salon wakarsa kasancewar akwai kurakurai da dama.
Lauyan ya ce sun fahimci cewa kalaman da mawaƙin ke amfani dasu akan shuwagabannin Kano sun fara tasiri musamman wajen ƙoƙarin bata kyakkyawar alakar dake tsakanin Katsinawa da Kanawa.
Katsina Post ta gano cewa daga cikin waɗanda ake zargin mawaƙin yaci mutuncin su a wakokin sa sun haɗa da Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, Tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Sanata,
Rabi’u Musa Kwankwaso, da kuma Ibrahim Shekarau.
Barrister Gandu ya tabbatar da cewa salon wakokin da mawaƙin ke amfani da su sun saɓa ma dokokin ƙasa domin sukan kawo tarzoma da fitina a ƙasa.
“Bayan cin karo da dokokin ƙasa, wakokin sun saɓa da koyarwar addinin Musulunci da al’adun mutanen jihar Kano”.
Haka kuma Lauyan yace sun rubuta takarda ɗauke da sako ga sarakunan da kuma gwamnatin jihar Katsina, da hukumar tsaro da neman a ja mashi kunne a matsayin shi na ɗan asalin jihar Katsina kuma talakan sarakunan.
Lauyan ya nuna takaici bisa wakar da Mawaƙin ya fitar a lokacin zaɓen Gwamna a Kano wanda tayi sanadiyar jawo cin mutuncin ga mahaifiyar mawaƙin da wasu ɓata gari su kayi.
Lauyan yayi fatan cewa matakin da suka ɗauka zai taimaka wajen dakatar da mawaƙin daga sake yin waƙoƙin cin mutunci ga shuwagabannin Kano kamar yanda suke zargi.
Katsina Post ta ruwaito cewa an samu wasu fusatattun matasa da laifin ƙona gida da ofishin mawaƙi Rarara dake Kano bayan ya fidda wata wakarsa da ake zargin yayi cin mutuncin ga tsahon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso da zaɓaɓɓen Gwamna, Abba Kabir