BANKWANA: Na yafewa kowa a jahar kano, nima ku yafe mini, Ganduje ga mutanen Kano
Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya roki al’ummar jihar da su yafe masa a yayin da ƙarshen wa’adin shekaru 8 na mulkinsa ke ƙarato wa.
Ganduje, wanda ya karbi mulki a shekarar 2015 a karkashin jam’iyyar APC, ya sake lashe mai cike da cece-kuce a 2019, inda ake sa ran zai mika mulki ga zababben gwamna, Abba Kabir Yusuf a karkashin jam’iyyar adawa ta NNPP.
Da ya ke jawabi a lokacin da ya ziyarci wurin tafsirin Alkur’ani a Masallacin Juma’a na Al Furqan, da ke Alu Avenue, Nasarawa GRA Kano a ranar Asabar, Ganduje ya ce “wa’adina na Gwamnan Jihar Kano ya zo karshe, kuma wannan sakon ban kwana ne.
“Ina yi muku fatan alheri, ga wadanda muka ɓatawa, ku gafarta mana, a nawa bangaren na yafe wa duk wadanda suka ɓata mini, na kuma yafe wa kowa da kowa a kan duk abin da ku ka fada a kaina, don haka ina neman gafarar ku.
“Yin afuwa ya na daga cikin kyawawan halaye a Musulunci. Yanzu babban Malami ya gama magana ne kan falalar tafiya, don haka ya kara da cewa “kamar yadda shugaban wannan masallaci ya yi jawabi, afuwa tana da matsayi mafi girma a cikin addininmu.
“Yafiya na daya daga cikin kyawawan dabi’un Musulunci, don haka ina neman gafarar ku kamar yadda nima na yafe wa kowa,” in ji Ganduje.