Shuaibu Lawan Kumurci Ya Sake yin Aure, Shekaru 18 bayan rasuwar Balaraba.
Fitaccen ɗan wasan Hausa, Shuaibu Lawan Kumurci ya angwance da falleliyar matarsa ayau, bayan aƙalla shekaru goma sha takwas 18, da rasuwar tsohuwar matarsa Balaraba.
Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Shu’aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci ya angwance da zukekiyar amarya A hotunan da Ahmed Gandujiyya ya wallafa a shafinsa ya ce Kumurci ya taba auren wata ta rasu bayan Balaraba.
Allah ya yi wa tsohuwar matarsa Balaraba rasuwa ne bayan da aka daura aurensu kuma ana kan hanyar kai ta dakin angonta Kumurci
Babu shakka mutuwa dole ce, tunda Allah ne ya tabbatar da cewa kowacce rai sai ta dandana zafinta.
Masana’antar fina-finan Hausa wacce aka fi sani da Kannywood, ta dandana rashe-rashe da dama.
Daga ciki kuwa akwai na ‘yan matan masana’antar wadanda suka shahara.
Ga wasu daga cikin ‘yan matan masana’antar da suka rasa rayukansu da kananan shekarunsu: 1.
Fadila Muhammad: Fitacciyar jarumar masana’antar fina-finan hausa wacce ta yi sharafi daga shekarar 2011 zuwa 2014, ta rasu a ranar 29 ga watan Augustan 2020 bayan gajeriyar rashin lafiya.
Tana daya daga cikin jarumai masu matukar salo da farin jini a masana’antar.
Matashiyar jarumar tana da wani irin salo na bayyana a wasan kwaikwayo, wanda ke saka zukatan masu kallo cikin nishadi.
Tauraruwarta ta fara haskawa tun bayan da ta fito a fina-finai masu suna Hubbi da Basaja.
Babu shakka wadannan fina-finan sun saka sunanta ya dauku ga ma’abota kallon fina-finan Hausa.
Babu shakka za a ci gaba da tunawa da ita matukar za a ambaci tarihin masana’antar fina-finan. Ta rasu tana da shekaru 27 a duniya.