News

IKON ALLAH: An Samu Wata Zuri’ar Da Da Zarar Sun Kai Shekara 18 Sai Su Kamu Da Cutar Mutuwar Jiki (Faralayiz) A Jihar Nasarawa

IKON ALLAH: An Samu Wata Zuri’ar Da Da Zarar Sun Kai Shekara 18 Sai Su Kamu Da Cutar Mutuwar Jiki (Faralayiz) A Jihar Nasarawa

Daga Aliyu Ahmad

Babu shakka Allah shine mai yin yadda Ya so kuma a duk lokacin da Ya so.

Wata zuri’a a garin Gitata dake karamar Hukumar Karu ta jihar Nasarawa, sun tsinci kan su cikin wata jarabta ta Allah wadda da zarar su kai shekaru 18 a duniya za su kamu da ciwon mutuwar sassan jiki (faralayiz). Inda ba za su kara iya wani aiki da gabobinsu ba, komai saidai a yi musu.

Zuri’ar wanda su bakwai ne suke a raye, yanzu haka kusan shida daga cikin su ba sa moruwa, inda ‘yar autar su daya tilo da take da lafiya ita ke dawainiya da su.

Kasancewar zuri’ar suna bukatar taimakò ga ahi kuma sun kasance marayu (ba su da uwa da uba), wanda hakan ya sa Gidauniyar Al-ihsan Foundation ta kai musu tallafin kayan abinci karkashin jagorancin Shugabanta, Ibrahim Bashir Ahmad (Ya Malam).

Gidauniyar ta Al-Hisan ta kuma baiwa wasu mabukata dake makwabta da marasa lafiyan da kayan abinci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button