BIDIYO: Hukuncin Kisan Da Kotu Ta Yankewa Abduljabbar Abin Farin Ciki Ne Ga Musulmai, Cewar Dakta Mansur Sokoto
Na saurari cikakken jawabin shari’ar alkali Ibrahim Sarki Yola yau da safe.
Shari’ar AbdulJabbar Kabara:
A bisa gaskiya alkalin ya nuna sanin makamar Shari’a da dokokin kasa, ga tsanaki da takatsantsan wajen bin diddigin matsalolin da aka gabatar masa tare da hukunce hukuncensu da gabatar da kowane irin hanzari da ake bukata.
A bisa zatona idan aka yi ma Shari’ar fassara mai kyau zuwa turanci babu wata kotu a Najeriya da za ta iya walwale ta.
Na gamsu kuma na yi farin ciki da samun irin wannan mataki na ilimi ga alkalan Shari’ar Musulunci a wannan kasa.
Allah ya kara inganta mana su, ya ba da ikon ci gaba da karfafar su tare da ba su horo da taimako ta kowace fuska.
Mansur Sokoto
24/5/1444H (18/12/2022)
Hukuncin Kisan Da Kotu Ta Yankewa Abduljabbar Abin Farin Ciki Ne Ga Musulmai, Cewar Dakta Mansur Sokoto