BIDIYO: Za Mu Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Wa Abduljabbar, Cewar Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Al-Haqqu
Wata ƙungiya ƙarƙashin ƙungiyar kare Haƙƙin ɗan Adam ta Alhaqqu ta bayyana shirinta na ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa da kotun shari’a ta yiwa Sheikh Abduljabbar Kabara bisa samunsa da laifin ɓatanci.
Yayin da yake jawabi ga manema Labarai yau Juma’a a Kano shugaban kungiyar Sa’id Bn Usman, yayi bayanin cewa ƙungiyar tana tattaunawa da iyalai da makusantan malamin kan batun, inda ya ƙara da cewa bayan haka sun yanke shawarar ɗaukaka ƙara domin tabbatar da adalci.
Yayi bayanin cewa ƙungiyar bata gamsu da hukuncin ƙaramar kotun ba.
Acewarsa an kammala shirin ɗaukaka ƙarar nan bada jimawa ba kuma za a sanar da al’umma.