Politics

Kwarewar Yaran Arewa A Fannin Karatun Kur’ani Da Kuma Hankalinsu Ya Nuna Cewa Za Su Iya Koyar Fasaha, Har Su Zama Tattalin Arziki Ga Kasa, Cewar Peter Obi

Kwarewar Yaran Arewa A Fannin Karatun Kur’ani Da Kuma Hankalinsu Ya Nuna Cewa Za Su Iya Koyar Fasaha, Har Su Zama Tattalin Arziki Ga Kasa, Cewar Peter Obi

Daga Hajiya Mariya Azare

A wata tattaunawa da aka yi da dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar LP, Mista Peter Obi a gidan talabijin na Arise, ya ce sanin littafin islama da yawancin yaran Arewa suka yi ya nuna cewa za su iya samun kwarewa akan hanyan fita daga kangin talauci.

“Idan har za su iya karatun Qur’ani hakan na nufin suna da hankali”, inji Mista Obi wanda kuma shine tsohon gwamnan Anambara a wani bangare na mayar da martani kan tunkarar ilmi. Inda ya da cewa zai sadu da su a inda suke koyon Kur’ani” kuma ya sanar da su cewa za su iya samun kwarewa.

“Ilmi a Arewacin Nijeriya ya koma baya tsawon shekaru da dama inda akasarin yaran da ba sa zuwa makaranta sun fito ne daga yankin Arewa bisa kidigdigan UNICEF.

Mista Obi ya sha bada shawarar cewa, ilmi a Nijeriya zai iya taka muhimmiyan rawa wajen fitar da kasar daga kangin talauci da rashi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button