BIDIYO: An saki Aminu Muhammad Adam Bayan Aisha Buhari Ta Janye Karar Da Ta Kai Akansa.
Kungiyar daliban jami’o’i ta Najeriya NANS, ta yi yekuwar fara zanga-zanga a ranar Litinin idan har ba a saki dalibin ba.
Rahotanni daga Najeriya na cewa uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta janye karar da ta shigar da Aminu Muhammad a kotu.
Uwargidan shugaban na neman kotu ta bi mata kadinta ne kan kalaman bata suna da take zargin Muhammad ya wallafa a kanta a shafinsa na sada zumunta.
A watannin baya, Muhammad ya wallafa wani sakon Twitter da ke cewa, “mama an ci kudin talakawa an koshi,” hade da hotonta.
Hakan ya sa a ranar 18 ga watan Nuwamba, jami’an tsaro suka kama Muhammad, dalibi a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa.
A ranar Talata aka gurfanar da shi a gaban kotu a Abuja, babban birnin Najeriya, lamarin da ya janyo suka daga sassa daban-daban na Najeriya.
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty ma ta yi Allah wadai da kama Muhammad.
Shi dai Muhammad ya musanta aikata laifin, kuma kotu ta tura shi gidan yari don jiran zaman kotu na gaba.
Sai dai bayanai da ke fitowa daga Najeriya a baya-bayan nan na nuni da cewa, Aisha Buhari ta janye karar.
Jaridar Daily Nigerian ta yanar gizo ta ruwaito cewa a ranar Juma’a mai shigar da kara Fidelis Ogbobe ya bayyana cewa Aisha ta janye karar.
Alkali Yusuf Halilu na babbar kotun tarayya a Abuja da ke sauraren karar, ya jinjinawa uwargidan shugaban kasar da ta yafewa Muhammad tare da janye karar kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito.
A ranar Alhamis kungiyar daliban jami’o’i ta Najeriya NANS, ta yi yekuwar fara zanga-zanga a ranar Litinin idan har ba a saki dalibin ba wanda ke shirin fara rubuta jarabawarsa ta kammala karatu.