Yanzu-Yanzu Gwamnatin Najeriya ta bukaci a gaggauta bude kamfanin simintin Dangote
Majalisar tsaro ta kasa karkashin jagorancin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ta bada umarnin bude masana’antar siminti na Dangote da ke Obajana a jihar Kogi ba tare da bata lokaci ba.
Majalisar ta bayar da umarnin ne a wani taro da ta gudanar a Abuja, babban birnin kasar.
Ministan harkokin ‘yan sanda, Mohammed Dingyadi, tare da takwaransa na cikin gida, Rauf Aregbesola da babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor, sun bayyana wa manema labarai bayan taron cewa fadar shugaban kas ace ta bayar da umarnin nan take.
Aregbesola ya ce an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kamfanin Dangote kan bukatar sake bude masana’antar simintin, inda ya bukaci bangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar.
Ministan ya kara da cewa majalisar ta ba da umarnin bude masana’antar nan take tare da ba da shawarar cewa a warware duk wasu batutuwan da ake takaddama a kai a bisa doka domin gwamnati ta himmatu wajen samar da ayyukan yi.