Yadda Wasu Mutum Hudu Gida Suka Mutu Bayan Kammala Cin Abinci, Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un
Rahotanni daga garin Mopa da ke jihar Kogi a Najeriya, na cewa wasu mutum hudu yan gida daya sun mutu, bayan kammala cin Amala.
Mutanen sun hada da mahaifi da ‘ya’yansa biyu mata, da kuma wani dan uwansu.
Kamar yadda rahotannin suka nuna mutanen sun kamu da rashin lafiya ne cikin dare, bayan kammala cin abincin.
Sai dai matar mutumin har yanzu tana jinya a asibiti.
Mai magana da yawun gwamnatin jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya fada wa BBC cewa an umurci jami’an tsaro da na lafiya da su fara bincike kan lamarin ba tare da bata lokaci ba.