BIDIYO: Allahu Akbar bidiyon Hira Da Yaro Me Basira Wanda Ya Gina Gadar Sama
Yan jarida sun samu yin hira da wani karamin yaro da ya kera gadar sama a Maiduguri, Jihar Borno, ya ce babu wanda ya koya mas yadda ake yi. Yaron mai suna Musa Sani Idris wanda gwamnan jihar, Babagan Umara Zulum ya dauki nauyin karatunsa ya ce ba zai bai wa gwamnan kunya ba.
Wannan yaro dai hotunansa sun karde shafukan sada zumunta a lokutan bayan wanda aka daukeshi lokacin da yake aikin gina gadar sama. Daga baya an samu labarin saukar nauyin karatunsa zuwa kasar waje.
A kwanan baya ne Zulum ya dauki nauyin karatun yaron bayan hotunan wata gadar sama makamanciyar wadda gwamnan ya gina. A wannan hirar da yaron da mahaifinsa suka yi da Aminiya, sun bayyana yadda ya fara kere-kere.
Abinda Ya Faru A Kwakin Baya
Karamin yaron nan da ya gina irin gadar sama da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya gina, ya ce burinsa shi ne ya zama injiniyan gine-gine.
Musa Sani mai shekara 13, wanda Zulum ya ba wa tallafin karatu na Naira miliyan biyar, ya yi amfani da laka ne ya gina irin gadar har da irin zanen da jikinta.
“Burina a rayuwa shi ne in zama injiniyan gine-gine in rika gina abubuwa domin ci gaban al’umma,” inji Musa.
Ya bayayana haka ne bayan Zulum ya dauki nauyin karatunsa zuwa hamshakiyar makarantar Golden Olive Academy da ke Maiduguri har zuwa kammala sakandare.
Dalibin, wanda yanzu mahaifinsa direban babur mai kafa uku ne ya bayyana wa Aminiya cewa, “Zan ba da himma a karatuna domin cika burina na zama injiniya.
“Wannan damar ba zan yi wasa da ita ba; Babban abin da zan mayar da hankali a kai shi ne karatuna, musamman ma ganin irin goyon bayan da nake samu daga mahaifana.”
Ga bidiyon hirar da Aminiya tayi da mahaifin yaron tare da shi kansa yaron:
Gidan su Musa
Kafin yanzu Musa dalibin yana aji hudun firamare ne a makarantar haddar Alkur’ani ta ‘Abba Kyari Qur’an Memorization and Integrated School’.
Makarantar tana nan a unguwarsu, Sabon Layi, Gwange, a garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Kafin yanzu, mahaifinsa, Malam Sani Idris, direban tasi ne, amma yanayin matsin tattalin arziki ya sa yanzu ya koma haya da babur mai kafa uku.
Da babur din yake kai Musa sabuwar makarantar da Zulum ya sa shi, yake kuma fadi-tashi nemo wa iyalinsa da ’ya’yansu bakwai abin sawa a bakin salati.
Yadda na gina Gadar Zulum da laka
Musa ya shaida wa Aminiya cewa wata rana sun je wurin da aka gina gadar ce sai ta ba shi sha’awa, da ya koma gida kuma sai ya yi amfani da laka ya gina irinta sak.
“Wata rana na je inda gadar saman take — wadda babu nisa da gidanmu a Gwange — sai na ga yadda aka tsara ta aka gina ta da titunan shiga gari.
“To sai abin ne abin ya burge ni, na yi sha’awar amfani da laka in gina irinta, Alhamdulillah, na gina ta sak, har da irin fentin jikinta,” inji shi.
Bayan ya gina gadar ce basirarsa ta dauki hankalin duniya, hotunansa suka rika tashe musaman a kafofin sada zumunta.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi takakkiya zuwa gidan su Musa, ya gane wa kansa gadar, ya kuma cika shi da mamaki.
Daga baya ya dauki nauyin karatun yaron daga aji biyar na firamare har zuwa kammala sakandare ya kuma biya kudin karatun.
Gadar sama da Zulum ya gina a daidai shahararren Shataletalen Kwastam da ke gairin Maiduguri, ita ce ta farko a Jihar Borno.
A watan Disamban 2021 Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ita, bayan Gwamnatin Zulum da ta kirkiro aikin ta kammala.
Sha’awar Musa da Gadar Sama
Dalibin ya shaida wakilinmu cewa tun yana dan kankani yake da sha’awar yin zane-zane da kuma amfani da laka wajen gina abubuwa.
“Na taso ne ina yawan sha’awar rubutu da zayyana da zane-zane da gina duk abin na gani ya ba ni sha’awa da laka.”
Babu wanda ya koya min
Ya ci gaba da cewa, “Babu wani a makaranta ko a wani wuri da ya taba koya min yadda ake zane ko yin abubuwa da laka.
“Ina ganin wannan baiwa ce Allah Ya yi min da zan iya ganin abu kuma in yi irinsa na laka ko ma in zana.
“Na gode Allah bisa wannan baiwa da kuma daukar nauyin karatuna da gwamnati ta yi domin ganin na samu ilimi mai nagarta.”
Ya kara da cewa, “Abin da ya ba ni kwarin gwiwar yin abubuwa da laka shi ne yadda nake son gina muhimman abubuwan more rayuwa da ake amfani da su a inda na taso.
“Saboda tsabar yadda nake son gadojin sama fiye da sauran gine-gine, in da kaina nakan kirkiri gadar sama da babu ita a ko’ina kuma in gina da laka.”
Dalibin ya yi godiya bisa tallafin karatun, yana mai cewa, “Na gode wa gwaman bisa wannan tallafi kuma ina tabbatar mishi cewa ba zan ba shi kunya ba, zan dage da karatu domin cika burina na zama injiniya.”
Tun kafin a sa shi makaranta ya fara
Mahaifin Musa ya ce Allah ne Ya yi wa dan nasa baiwar zane da gini da laka tun kafin a sanya shi a makarantar firamare.
“Zan iya tunawa ya fara yin wadannan abubuwa ne tun kafin ya kai shekara biyar haihuwa.
“Duk lokacin da ya samu takarda da abin rubutu za ka ga ya fara zana wani abin da ya gani a gida ko a cikin unguwa, daga baya kuma ya fara yin abubuwa na laka.
“Da na ga irin baiwar da Allah Ya yi masa na zane da yin abubuwa na laka ba tare da an koya mishi ba, sai na yi ta rokon Allah Ya ba ni karfin taimaka masa, in sanya shi a makarantar koyan sana’o’i domin bunkasa basirar tasa don cim ma burinsa,” in ji Malam Idris.
“Da Gwamna Zulum ya ga gadar sama da Musa ya gina da laka, shi da kansa tare da manyan jami’an gwanmati suka nemi gidanmu, ya dauki nauyin karatunsa domin habaka basirar tasa.
“Babu wanda ya koya mishi zane ko yin abubuwan, baiwa ce; talaka ne ni, amma Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya bakwai, ciki har da Musa.
“Babu abin da za mju ce wa Zulum sai addu’ar Allah Ya saka mishi, kuma za mu yi iya bakin kokarinmu wajen bai wa Musa kwarin gwiwa domin cikar burinsa.
“Ni da mahaifiyarsa mun riga mun tsara yadda za mu ba shi goyon baya,” kamar yadda Malam Idris ya bayya.
Wani malamin Musa a tsohuwar makarantarsu, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce Musa dalibi ne mai basira.
“Natsattse ne kuma yana da saukin kai da saurin fahimtar duk abin da aka koya masa,” inji malamin.