News

Bidiyon: Innalillahi.. Mutane Arba’in Sun Mutu Bayan Da Kwala-kwalen Da Ya Kwaso Su Ya Nutse A Kogin Benue

Bidiyon: Innalillahi.. Mutane Arba’in Sun Mutu Bayan Da Kwala-kwalen Da Ya Kwaso Su Ya Nutse A Kogin Benue

Rahotanni daga jihar Taraba ta Najeriya na cewa, ana fargabar mutuwar mutane akalla 40 bayan kwale-kwalen da ya kwaso su ya kife a kogin Benue.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta shaida wa RFI Hausa cewa, ya zuwa yanzu, an yi nasarar gano gawarwakin mutane 7, yayin da ake ci gaba da aikin neman sauran mutanen da suka nutse a kogin.

SP, Usman Abdullahi, shi ne Jami’in Hulda da Rundunar ‘Yan sandan jihar Taraba ya kuma shaida wa RFI Hausa cewa, lamarin ya faru ne a garin Ibbi bayan da katafaren kwale-kwalen ya yi dakon wata motar fasinja domin tsallkawa da ita.

A cewar jami’in ‘yan sandan, motar kirar Sharon ta taso ne daga birnin Jalingo da nufin zuwa Abuja, amma bisa al’ada, kwale-kwale kan yi dakon motoci domin tsallkawa da su kogin Benue kafin su ci gaba da balaguronsu da zarar sun isa Ibbi.

Wannan katafaren kwale-kwalen ya ci karo ne da wani tudu a yayin tafiyarsa a cikin kogin, lamarin da ya yi sanadiyar nutsewar motar da kuma sauran fasinjojin da ke zaune a cikin kwale-kwalen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button