Rundunar ‘Yan sandan Kasa Da Kasa Sun Chafke Sheikh Tukur Mamu A Masar Malamin Da Ya Shiga Tsakanin Gwamnati Da Yan Bindiga.
ranar Talata ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol suka kama Mamu a birnin Alkahira da ke Masar, a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa aikin Umrah a kasar Saudiyya tare da ahlinsa.
WASHINGTON D.C. —
Hedkwatar Hukumar tsaron farin kaya ta DSS da ke Abuja, ta tabbatar da kama Malam Tukur Mamu, tsohon mai shiga tsakanin gwamnatin Najeriya da ‘yan ta’adda a tattaunawa da aka yi kan sako fasinjojin jirgin kasa da aka sace a farkon shekarar nan.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a a hukumar, Peter Afunanya, DSS ta ce ta kama Mamu ne don ya amsa wasu tambayoyi da ke da nasaba da tsaro.
“Muna masu sanar da cewa, abokanan huldar Najeriya a fannin tsaro na kasashen ketare, su suka kama Mamu a birnin Alkahira a ranar 6 ga watan Satumba, 2022, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.
“Daukan wannan mataki ya biyo bayan bukata da rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro da na tattara bayan sirri, suka mika ga abokanan hulda a kasar waje na a maido da shi zuwa Najeriya, don ya amsa wasu muhimman tambayoyi kan binciken da ake yi game da tsaro a wasu sassan kasa.” Afunanya ya ce cikin sanarwar da Muryar Amurka ta samu kwafi.
Muryar Amurka ta ruwaito yadda a ranar Talata ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol suka kama Mamu a birnin Alkahira da ke kasar Masar, a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa aikin Umrah a kasar Saudiyya tare da ahlinsa.
Hukumar ta DSS ta kama Malam Mamu ne a ranar Laraba bayan da ya sauka a jirgin kamfanin Egypt Air a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano da ke jihar.
Gabanin a maido da shi kasarsa, sai da aka tsare shi tsawon sa’a 24 a birnin na Alkahira a cewar rahotanni.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mamu yana cewa ba ya fargabar komai domin bai aikata wani laifi ba.
“Ba na fargabar komai.” Mamu ya fadawa jaridar a wata hira ta musamman da ta yi da shi.
Tun da farkon kama shi a Masar, Alkali Mamu, kani ga tsohon mai shiga tsakanin ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa an tsare yayan nasa a Alkahira.
Mamu, wanda shi ya mallaki jaridar Desert Herald, ya taka rawar ta hanyar shiga tsakanin ‘yan bindiga da gwamnatin tarayya wajen sako wasu daga cikin fasinjojin da aka sace a jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris.
A baya, an taba zarginsa da alaka da ‘yan ta’addan duba da irin rawar da ya taka wajen sako fasinjojin, zargin da ya sha musantawa.
A wata hira da ya yi ta musamman da Muryar Amurka a watan Yuli, Malam Mamu ya ce ba zai iya ci gaba da shiga tsakani a tattaunawar sako ragowar fasinjojin ba, saboda abin da ya kira barazana da ake yi wa rayuwarsa.