News

BIDIYO: Yadda Sojojin Da Ake Zargi Da Kisan Sheikh Aisami Suka Amsa Laifinsu A Gaban Yan Sanda – ‘Yan sanda

BIDIYO: Yadda Sojojin Da Ake Zargi Da Kisan Sheikh Aisami Suka Amsa Laifinsu A Gaban Yan Sanda – ‘Yan sanda

A ranar Juma’ar da ta gabata aka kashe Sheikh Aisami a kusa da unguwar Jaji Maji a karamar hukumar Karasuwa da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya kamar yadda rahotanni suka nuna.

Sojojin Najeriya biyu da ake zargi da kashe Sheikh Goni Aisami Gashua, sun amsa laifin aikata kisan malamin a jihar Yobe bayan da ‘yan sanda suka kama su.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Yobe ta kama sojoji biyu inda ake tsare da su ake ci gaba da tuhumarsu kan kisan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkareem ne ya tabbatarwa da jaridar Premium Times, cewa sojojin sun amsa laifin kashe fitaccen malamin.

Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a yanar gizo ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sanda jihar ta Yobe ta bayyana sunayen sojoji da ake zargi a matsayin Lance Corporal John Gabriel da Lance Corporal Adamu Gideon, wadanda suke aiki da bataliya ta 241 a Nguru a jihar ta Yobe.

A ranar Juma’ar da ta gabata aka kashe Sheikh Aisami a jihar ta Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya kamar yadda rahotanni suka nuna.

Daya daga cikin sojojin ya nemi Sheikh Aisami ya rage masa hanya inda malamin ya amince, daga bisani sojan ya kashe malamin ya yi yunkurin tafiya da motarsa, amma motar ta ki tashi.

Sheikh Aisami na hanyarsa ta komawa Yobe ne daga jihar Kano a lokacin da sojan ya nemi ya rage masa hanya.

Rahotannin sun ce daga baya sojan ya kira wani abokinsa, wanda ya zo da wata mota daban, amma ita ma ta ki tashi bayan isarta wurin.

Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan vigilante ne suka kama su a lokacin da suka je don su taimakawa sojojin wajen janyo motocin nasu.

A halin da ake ciki rundunar sojin Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin inda ta ce ta hada kai da rundunar ‘yan sandan jihar Yobe don gano asalin abin da ya faru.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button