Bidiyon Yadda Fitacciyar Jarumar kasar Ghana, Akuapem Poloo Ta Karbi Addinin Musulunci
Fitacciyar Jarumar kasar Ghana mai suna Akuapem Poloo ta bar addinin Kiristanci inda ta karbi Addinin Musulunci.
Poloo da kanta ce ta sanar da labarin Musuluntar tata a shafinta na soshiyal midiya Masoya da mabiyanta sun tayata murnar karbar kalmar shahada da ta yi sannan sun yi mata fatan alkhairi a sabon addininta.
Shahararriyar jarumar kasar Ghana Rosemond Alade Brown wacce aka fi sani da Akuapem Poloo, ta karbi addinin Musulunci.
Poloo ta Musulunta ne a ranar Talata, 9 ga watan Agusta, bayan ta yi kalmar shahada tare da kadaita Allah.
Jarumar da kanta ce ta sanar da labarin Musuluntar tata a shafinta na Instagram inda ta wallafa hotunan dan kwarya-kwaryan taron da aka shirya na Musuluntarta tare da wasu malamai. Tuni mabiyanta suka shiga sashin sharhi domin tayata murna tare da yi mata barka da zuwa cikin addinin Musulunci.
Ga yadda ta rubuta a shafin nata: “Alhamdulillah na zama cikakkiyar Musulma yanzu godiya ga mataimakin limamin ASWAJ Ga West da babban limamin Nsakina Quran Reciter da ahlinsa kan taimakawa da suka yi wajen yiwuwar hakan ”
Masha Allah