Sunyi Aure Bayan Ta Fara Tura Masa Da Sako A Shafinsa Na Instagram Shekara Biyar Da Suka Wuce.
Daga Shuaibu Abdullahi
Wata Budurwa ta shelanta cewar da kanta ta fara yiwa matashin magana a Kafar Instagram shekaru biyar baya da suka wuce, yanzu gashi har an daura musu Auren sunnah.
Ta wallafa hakan ne a shafinta na Instagram tare da hotunan daurin Auren ta ita da Mijin nata, kuma a dukkan alamu Aure ne na Soyayyah, kuma mai cike da alfahari.
Wallafar bata bayyana cikakken sunan Budurwar ba sai dai an saka (Mrs. Adda_Tee).
Wannan na zuwa ne bayan da Malamai suke kara wayar da kan al’umma musamman mata kan cewa mace zata iya bayyana soyayyar ta ga Namijin da take so Mai Kamala da mutunci ko kuma Mahaifin yarinya zai iya samarwa yarinya miji da kan sa ba tare da yaji na’uyin hakan ba.
Sai dai har yanzu mata da al’adar arewaci suna ganin zubar da mutuncin mace ne ta gayawa Namiji tana son sa da sunan Aure, suna tunanin hakan zai iya jawo rai ni da zubar da girma.