BIDIYO: Saratu Mai Baiwar Lissafi A Kano Ta Samu Tallafin Karatu Daga Bankin Duniya
Bankin Duniya ya dauki nauyin karatun Saratu Garba, yarinyar nan mai shekara 11 mai baiwar lissafi a kauyen Gwadayi na karamar hukumar Gaya a jihar Kano.
Malam Aliyu Musa, Jami’i Yada Labarai na shirin ne ya bayyana haka ga Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba.
Saratu ta samu tallafin ne a karkashin shirin tallafawa mata don su yi ilimi (AGILE), wanda Bankin ke daukar nauyi a jihar Kano.
Malam Yusuf, wanda kuma shi ne Mataimakin Daraktan yada labarai na Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ya ce, ofishin kula da shirin na Bankin Duniya a jihar Kano ya bayar da umarni a zakulo yarinyar nan a kuma sa ta a makaranta.
“Sai aka yi sa a, masu kula da shirin ilimin mata na AGILE na tsaka da ziyara zuwa masarautu biyar na jihar Kano don neman hadin kan sarakuna kan batun ilimin mata a jihar,” in ji shi.
A yayin ziyararsu a masarautar Gaya ne jami’an suka yi wa Sarki bayanin yarinyar da kuma aniyarsu ta daukar nauyin karatunta, sai Sarkin na Gaya ya sa aka zo da yarinyar da kuma iyayenta har gabansu.
Nan take wakilin a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano, Malam Haruna Mohammed Pandau, ya ba Saratu kayan makaranta da jakar makaranta da kuma wasu kayayyakin karatu.
Shi kuma Ado Tafida Zango, mai kula da shirin AGILE a jihar, ya ba ta Naira 20,000 daga aljihunsa don taimaka wa karatun nata.
Kafin yanzu dai akwai wani dan siyasa, tsohon hadimin Shugaba Buhari, Bashir Ahmad da Gidauniyar Farfesa Adamu Gwarzo da suka dauki nauyin karatun Saratu tun daga Firamare har zuwa Jami’a da kuma tallafa wa iyayenta da kudade sana’a da kayan abincin bayan bayyanar bidiyon da ya fito da baiwarta da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani.