BIDIYO: Motocin Da Shugaban Kasa Buhari Ya Amince Zai Baiwa Jamhuriyar Nijar Gudunmawa Wanda Kudin Su Yakai Naira Biliyan Daya Da Miliyan 400
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sayo tare da bayar da gudunmawar motocin da kudinsu ya kai Naira biliyan daya da miliyan 400 ga makwabciyar kasar Jamhuriyar Nijar.
Ministar kudi, da tsare-tsare ta kasar, Zainab Ahmed, ta shaida wa manema labarai bayan taron majalisar zartaswa da aka yi a ranar Laraba cewa, tallafin da aka bayar na taimakawa kasar Nijar ne don magance matsalolin tsaro.
Ta ce irin wannan gudummawar da Najeriya ke bayarwa ga makwabtanta ba sabon abu bane.
Zainab Ahmed ta ce hakki ne na shugaban kasa ya dauki irin wadannan matakai bayan ya yi nazari sosai kan lamarin.