DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Kashe Hanifa Abubakar
Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke hukuncin kisa kan Abdulmalik Tanko kan samun sa da laifin kashe dalibarsa Hanifa Abubakar.
Mai Shari’a Usman Na’abba da ke jagorantar ƙarar ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis 28 ga watan Yulin 2022.
Ana zargin malaminta Abdulmalik Tanko ne ya sace ta a watan Disambar 2021 tare da kashe yarinyar mai shekara biyar, kana ya binne gawarta a gidansa.
Kisan nata ya ja hankalin duniya inda dubban mutane, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, suka yi tur da shi.
Bayanai sun tabbatar da cewa wasu mutane ne suka ɗauke ta a babur mai kafa uku da ake kira A-Daidaita-Sahu bayan ta dawo daga makaranta a kan hanyarta ta zuwa gida inda suka tafi da ita.
An yi ta nema da cigiya amma sai bayan kwana 46 aka ji ɗuriyarta.
A watan Janairu ne aka gano gawar yarinyar da aka sace a ranar 4 ga watan Disambar 2021.
‘Yanda sanda sun tono gawarta tata wadda ake zargi Abdulmalik Tanko, mai makarantar Noble Kids Academy, ya binne a wani rami.
An zarge shi da hada baki da Isyaku Hashim da matarsa Fatima Jibril da laifukan da suka hada da hada baki wajen aikata laifi, da satar mutum da kuma tsare yarinyar da suka sace ba tare da amincewarta ba da kuma kisan kai.
An kwashe kimanin watanni shida ana shari’ar wadda Mai Shari’a Usman Na’abba yake jagoranta.
An fara zaman kotun a karkashin Mai Shari’a Usman Na’abba.
Tuni aka gabatar da wadanda ake zargi su uku a gaban kotun.
Barista Musa Lawan, Kwamishinan Shari’a na Kano, shi ne ke jagorar lauyoyin gwamnati.
Ita kuma Barista Asiya Mohammad tana jagorantar lauyoyin da ke kare Abdulmalik Tanko da sauran mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Hanifa Abubakar.